1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

090610 Israel Hamas Tauziehen

June 9, 2010

Isra'ila na ƙara fiskantar matsi kan ta bari abinciki harin da ta kaiwa 'yan fafitakar buɗe zirin Gaza

https://p.dw.com/p/NlyU
Jiragen ruwa ɗauke da masu kai agaji a GazaHoto: AP

Har izuwa yanzu dai ƙasar Isra'ila na ci gaba da ƙin amincewa da kafa wani kwamiti mai zaman kansa daga ƙetare, wanda zai binciki kisan masu kai kayan agaji da sojin ta suka yi, wanda kuma ya jawowa ƙasar ta Yahudawa tofin Allah tsine daga duniya. 

Izuwa yanzu dai idan ka duba kudancin birnin Ƙudus babu abinda za ka gani illa kayan agajin wanda ƙungiyoyi suka shirya kaiwa Gaza, wanda kuma yake zube a filin Allah, kayan kuma ya haɗa da kujerun kuragu, da takalma, da jakunan 'yan makaranta, wanda dama ake son kaiwa Palsaɗinawa a Gaza, yankin da Isra'ila ta datse. To amma har yanzu tun wancan lokacin da sojin ruwan bani Yahudu suka farma jiragen da ke dakon kayan, babu abinda ya isa Gaza.

 Ita dai Ƙungiyar Hamas dake iko da zirin Gaza ta ƙi amincewa da buƙatar Isra'ila, na cewa sojinta za su kai kayan. Manjo Orel Rome shine jami'in sojan Isra'ila da aka ɗorawa nauyin isar da kayan da suka ƙwaci daga ƙungiyoyin fafitikar buɗe yankin na Gaza.

"Wacan kayan da kake gani, agaji ne da ake kaiwa a duk rana. Matsalar tana daga Palasɗinawa ne, amma abune da muke son dubawa, domin ganin wannan kayan agajin ya isa kamar yadda ƙungiyoyin fafitikar suka nema, kuma abinda muke yi a kullum"

Kimanin tireloli hamsin aka loda da kayan wanda Isra'ala ta ƙwace daga ijragen ruwan, amma har yanzu haka motocin suna tsaye, babu wani kayan da ya isa inda aka nufa. Tun shekaru uku da suka gabata dai Isra'ila take hana duk wani kayan agaji shiga zirin Gaza, sai dai wanda yake cikin jerin amintattatun kayan da sojinta suka yarda ne kawai zai iya wucewa.

Kakin sujan Hamas dake zirin Gaza Abu Zuhri ya dorawa Isra'ila laifi na rashin isar da kayan.

"Wannan kayan agajin da ƙungiyo masu fafitikar karya datsewar da aka yi wa Gaza suka kawo, ba mu ne muka shirya shi ba, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama ne suka tsara shi, to kuma wa yake da 'yancin isar da shi ga masu buƙata. Yanzu ana tattaunawa tsakanin waɗanda suka shirya kawo kayan, ta yadda za'a isar da shi ga mabuƙata. Mu a ƙungiyar Hamas ba mune muka kawo kayan ba, don haka ba za mu iya hanawa ko barin a shigo da shi ba"

Rohotonni sun bayyana cewa tun a shekara ta 2007 akwai kimanin kayakin daban daban har dubu huɗu, wanda suka haɗa da siminti da wasu kayan gini, wanɗanda Isra'ila ta hana a shirgar da su Gaza kuma suna jibge yanzu haka. Shugaban kula da aikin agaji a Gaza Ali Al'Nazil yace

 Mun yanke shawarar hana masu mamaya yin yadda suke so da wannan kayan, don haka mukace idan dai sai Isra'ila ta tantance abinda take so ya shigo, to ta bari ta riƙe kayan. Yahudawan da kansu sun rusa mana gidaje, da asibitoci da masana'antu, amma yanzu suce wai ba za su bari a shigo mana da kayan gini ba, don haka su bar ɗaukacin kayan ya shigo nan Gaza kawai"

Yanzu haka dai babban sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban ki-moon ya yi ƙira ga Isra'ila, da cewa dolene ta bar wani kwamiti mai zaman kansa daga ƙetare, ya binciki yadda aka yi har sojin Isra'ilan suka shiga tekun ƙasa da ƙasa suka hallaka masu kaiwa Palasɗinawa agaji.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Clemens Verenkotte

Edita: Umaru Aliyu