1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hana yancin fadan albarkacin baki a Turkiya

Hauwa Abubakar AjejeDecember 28, 2005

A yanzu haka ana tuhumar wani fitaccen marubuci da yan jarida saboda kalubalantar gwamnati

https://p.dw.com/p/Bu2w
Orhan Parmuk
Orhan ParmukHoto: AP

Marubuta da masana ilmin zamani da mawaka kimanin su 169 na kasar Turkiya suka sanya hannu suna kalubalantar sashe na 301 na kundin shariar kasar Turkiya wanda a karkashinsa ne sanannen marubucin kasar Orhan Parmuk da wasu marubutan kasar da dama suke fuskantar dauri zama gidan kurkuku.Daya daga cikin wadanda suka sanya hannu kan wannan kara kuwa shine Sanar Yurdatpan,wani mawaki wanda yace,yanzu lokaci yayi da zaa kawo sauyi a tsarin shariar kasar.

“bamu da lokacin da zamu bata don wannan batu,yadda ake murda dokar kasa kamar haka,amma kuma idan har babbar kotu taci gaba da bin wannan tsari,to zai yi wuya a canza shi,watakila zamu ci gaba da kalubalantar dokar nan da shekaru 10 zuwa 15 masu zuwa”

Abin mamaki anan shine,a farkon wannan shekara ne aka bullo da sashen dokar na 301,a matsayin wani bangare na gyaran fuska da gwamnati tayiwa tsarin shariarta,domin cika sharuddan shiga Kungiyar Taraiyar Turai.

Sashen na 301,ya tanadi cewa,babban laifi ne,mutum ya kaskantar da asalin Turkawa.wannan kuwa ya sanya an tsare yan kasar da dama.Hiiant Dink,editan wata jaridar Turkiya da Armenia,yana daya daga cikin wadanda aka fara tuhuma bisa wannan sashen doka,batu da har yanzu yake daukaka kara a kai,ya kuma halarci zaman kotun na shariar Pamuk,ya kuma kalubalanci shariar da ake gudanarwa akai.

“ina mai bakin cikin yadda kasata ta kasance.wannan abin kunya ne a garemu baki daya.ya kamata mu zauna mu duba yadda muka kasance cikin wannan hali.ya kamata gwamnati tayi tunani akan wannan,ya kamata kuma Kungiyar Taraiyar Turai tayi tunani akai”

Yanzu haka Dink yana fuskantar sharia karkashin dokar ta 301,saboda ya kalubalanci tsarin shariar Turkiya.

Hakazalika,ana ci gaba da binciken shugaban wani kanfani,bisa laifin kalubalantar tsarin dokar kasar.

Yayinda shi kuma Pamuk,a cewar masu buga littafansa,ana kuma bincikensa game da hira da yayi da wata jaridar Jamus,inda yayi suka ga rundunar sojin kasar.

Shariar da ake gudanarwa a yanzu,tana barazana ga kokarin kasancewar Turkiya memba ta Kungiyar Taraiyar Turai.Shugaban komitin majalisar Turai kan Turkiya,Joost Lagendyke yace ba zai yiwuwa wannan hali yaci gaba ba.

“muddin ana samun matsaloli irin wannan,to fa zaa dakatar da dukkan tattaunawar shigar Turkiya kungiyar,saboda Turai zata ce ba zamu iya tataunawa da kasar da inda a kowane mako take gurfanar da mutanenta dabam dabam gaban kotu ba.”

Lagendyke da kansa,ana bincikensa saboda lafin kalubalantar rundunar sojin Turkiya.Amma duk da wannan hali da ake ciki wasu masu tofa albarkacin bakinsu suna ganin cewa kamar wasan kwaikwayo ne gwamnati takeyi na kin amsa kiraye kiraye da akeyi mata.

Prime minister Recep Tayyib Erdogan yaki yarda a lokuta da dama yayi kwaskwarima ga wannan sashen doka da ake takaddama akansa,yana mai fadin cewa matsalar tana a bangaren alkalai ne ba dokar ba.

Wannan tsatsauran matsayida ya dauka,ana ganin kamar neman kwantar da hankulan bangarorin addini da masu kishin kasa na jamiyarsa ne wadanda suke zarginsa da yin sasauci ga Turai,game da batun shigarsa kungiyar.Kodayake ana ci gaba da yada jita jitar cewa,zaayi watsi da shariar Pamuk kafin watan fabrairu da zaa koma bakin shariar.

Sai dai kuma baa san makomar sauran marubuta da basuyi fice kamar Pamuk ba,da yan jarida da suke fuskantar shekaru zuwa kusan 3 a gidajen yari saboda kawai sun baiyana raayoyinsu.