1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hungari ta mika Horst Mahler ga kasar Jamus

Gazali Abdou Tasawa
June 13, 2017

Hukumar 'yan sandar Hangari ta mika wa Jamus Horst Mahler dan ta'addar nan mai akidar karyata kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa wanda ya gudu bayan da kotu ta yanke masa hukuncin zaman kaso.

https://p.dw.com/p/2edls
Ungarn Auslieferung Horst Mahler an Deutschland
Hoto: picture-alliance/AP Photo/MTI/Z. Mihadak

Hukumar 'yan sandar kasar Hangari ta sanar da mika wa mahukuntan Jamus Horst Mahler dan ta'adda dan kasar ta Jamus mai akidar karyata kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa kana daya daga cikin jagororin kafa sabuwar Kungiyar masu ikidar kwamunisanci da ya rikide zuwa dan Nazi, wanda 'yan sandar kasar ta Hangari suka kama a cikin watan Mayun da ya gabata. 

An mika wa mahukuntan kasar ta Jamus mutumin a wannan Talata a filin jiragin sama na Budapest, inda daga nan ne wani jirgin saman Jamus zai dauko shi zuwa kasar ta Jamus. 

A shekarar 2009 wata kotun kasar Jamus ta yanke wa Horst Mahler hukuncin zaman kaso na shekaru shida bayan da ta same shi da laifin karyata kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa a lokacin mulkin 'yan Nazi, amma kuma ya tsere zuwa Hangari.