1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hangari ta dauki mataki a kan 'yan gudun hijira

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 11, 2015

Kasar Hangari ta sanya dokar ta baci a kan batun 'yan gudun hijira domin kare kanta daga kwararar bakin haure.

https://p.dw.com/p/1GVAs
Firaministan Hangari Viktor Orban
Firaministan Hangari Viktor OrbanHoto: Reuters/B. Szabo

Firaministan kasar Hanagari Viktor Orban ya ce in har dokar ta bacin da kasarsa ta sanya a kan bakin haure da 'yan gudun hijira ta fara aiki to duk dan gudun hijirar da suka samu za su cafke shi nan take kuma zai fuskanci tuhuma a masatyin wanda ya yi musu kutse a kasarsu, yana mai cewa ba zasu iya jurewa dawainiyar 'yan gudun hijirar baki daya ba. Orban ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin Budapest, inda ya dora alhakin kwararar 'yan gudun hijirar zuwa kasarsa a kan Girka. Ya kara da cewa in har Girka ba za ta kare kan iyakarta ba to su za su kare tasu. Hangari dai ta bar dubbban 'yan gudun hijira sun bi ta kasarta zuwa kasashe masu karfin tattalin arziki da suke burin shiga irinsu Jamus da Seweden, sai dai ta ce za ta gina shinge a tsakaninta da Sabiya cikin watan Oktoba mai kamawa domin kare kasarta daga kwararar bakin hauren.