1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hannayen jari a Girka sun fara farfadowa

Yusuf BalaAugust 6, 2015

A cewar masu kula da hada-hadar hannnayen jarin na birnin Athens darajar hannayen jarin bankunan kasar da ma na wasu kasashen Turai na samun tagomashi.

https://p.dw.com/p/1GBI9
Griechenland Wiedereröffnung Börse Athen
Kasuwar shinku a AthensHoto: Getty Images/AFP/A. Messinis

Hannayen jari a kasar Girka a ranar Alhamis din nan sun fara samun daidaito a daidai lokacin da shirin bai wa kasar tallafi a karo na uku ke ci gaba da kankama.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki hudu bayan bude kasuwannin shinku a kasar bayan da aka rufesu tare da bankunan kasar. A cewar masu kula da hada-hadar hannnayen jarin na birnin Athens darajar hannayen jarin bankunan kasar da ma na wasu kasashen Turai na samun tagomashi.

A cewar hukumar kungiyar ta Tarayyar Turai tattaunawar da ake yi da mahukuntan na Girka ana samun ci gaba kafin akai ga matsaya ta karshe da ake son cimmawa a ranar 20 ga watan nan na Agusta.

Mina Andreeva ita ke magana da yawun hukumar kuma ta yi karin haske kamar haka:

Ta ce "Abin da shugaban hukumar kungiyar ta Tarayyar Turai Jean Claude Junker da kansa ya bayyana a ranar Laraba a tattaunawar da aka yi da shi har yanzu shi ne abin da aka tabbatar, tattaunawa da mahukuntan kasar Girka ana samun ci gaba".

Mahukunatan hukumar dai na da kwarin gwiwa kan sharudan da suke cimmawa sannu a hankali da mahukuntan na birnin Athens.