1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hanyar aikewa da sako a rubuce na Twitter

May 31, 2009

Hanyoyin sadarwa na zamani acikin sauki

https://p.dw.com/p/I19H

Twitter, wani tsari ne na aikewa da sakon SMS, wanda yake tafiya kai tsaye zuwa internet, a lokaci guda kuma ya isa ga wayoyin daruruwan mutane wadanda kake da adireshinsu a wayarka. Wannan tsari na aikewa da sakon ta hanyar Twitter ya zama wata hanya ta kwato yancin al'umma da kuma yancin fadin Albarkacin baki a fadin duniya. A kasar misra ma ana kallon wannan tsari a matsayin wata jam'iyyar adawa mai zaman kanta.

A ranar 10 gawatan Afrilun 2007, lokacin da yan sandan kasar Misra suka cafke wani Ba'amirke dan jarida mai suna James Buck, yana cikin ɗaukar hoton wata zanga-zanga da ake yi a ƙasar, suka kuma jefa shi a bayan kanta, ba su taɓa yin la'akari da cewa, akwai wani tsari mai suna twitter ba.

Tun kafin a cafke Buck, sai ya faki idon 'yansandan ya lalubo wayar salularsa, sai ya rubuta 'an kama ni'. ya kuma aika ta sakon SMS. Kasan cewar Buck yana amfani da tsarin Twitter, kafin kace kwabo sako ya bazu a internet da kuma wayoyin salular mutanen da Buck din yake da adireshinsu.

Nan da nan kuwa sai yan uwa da abokan arzkin Buck da suke a Amirka da ma na ƙasar ta misra, suka shiga zanga-zanga da kiran a sake shi.

Sai ga shi washe kari an saki James Buck, bayan da jami'arsa ta tura wani lauya, tare kuma da wayar tarho da mahukuntan Amirka suka yi wa takwarorinsu na Misra akan cewa a sake shi. Godiya ga tsarin Twitter.

Gadai abin da wani mutum Bamisre, mai amfani da tsarin na Twitter yake cewa;

"Ya ce, matsalar da muke fama da ita a Misra ita ce, da zarar mutane sun fito domin fadin albarkacin bakinsu ko kuma nuna adawa da wasu manufofi na gwamnati, sai kaga jami'an tsaro suna cafke mutane ba sani ba sabo. Sai ai ta neman mutum a rasa. A she yana can a tsare. Don haka yanzu wannan tsari na Twitter ya taimaka wajen sanar da duniya sirrin da ba za ka iya fitowa fili ka faɗa ba."

Ta amfani da wannan tsari na Twitter da James Buck ya yi ne, nan da na sako ya isa ga lauyoyi da masu fafutukar kare bil Adama, da yan jarida, inda batun na Buck ya zama kanun labaran jaridun Amirka, ko wacce jarida ka daga sai ka ga an rubuta baro.baro " Jami'an Misra sun cafke James Buck":

Adai cikin watan Afrilun na shekara ta 2007, sai da wani abu ya sake faruwa, inda kungiyar ma'aikata ta kasar misra, ta gayyaci taron zanga-zangar lumana domin yin yajin aiki saboda wasu bukatu da suke so daga gwamnati. Anan ma sai da 'yansanda suka caccafke mutane. Inda wasu da dama aka sako su, bayan da suka rika aikewa da sakon sms na "An kama ni":

Amr Gharbeia, wani masanin harkokin fasahar sadarwar intanet ne a kasar ta Misra,

Ya ce "A kwai lokacin da aka kama wani abokinmu ɗan gwagwarmayar gwato yanci, saboda wata zanga-zanga da aka gudanar, yana cikin mota kawai suka kama shi. Ta hanyar Twitter mutane sukai ta aikewa da sako, na motar da ta kamashi, da lamabar motar dama inda motar ta kai shi, sakamakon haka dole ta sa aka sake shi"

Tun daga lokacin da aka cafke James Buck a Misra, ake amfani sakon "An kama ni" a matsayin salon magana dake nuna cewa, jami'an tsaron Misra sun tsare wani mutum.


Mawallafi: Abba Bshir

Edita: Zainab Mohammed