1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

hanyar karkashin kasa ta kasar Ingila da Faransa

Abba BashirFebruary 6, 2006

Tarihin hanyar karkashin kasa ta kasar Ingila da Faransa

https://p.dw.com/p/BvVZ
The Channel Tunnel
The Channel TunnelHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon, ta fitone daga hannun Malam Mudassir Abdurrahman Mazauni a birnin kanon dabon tarayyar Najeriya.Malamin yace don Allah ina so ku bani tarihin shararriyar gadar nan da aka haka ta garkashin-kasa daga kasar Ingila zuwa kasar Faransa, wadda ake kira da Turanci “The channel Tunnel’’

Amsa : To malam Mudassiru, hanyar karkashin kasa wadda aka gina daga kasar Ingila zuwa kasar Faransa , wadda aka fi sani da suna“The channel Tunnel’’ a Turance, an kammala gina ta ne a shekarar 1994 kuma an yi bikin bude ta domin zirga-zirgar fasinja a wanna shekara.

kamar dai yadda wani marubuci bafaranshe mai suna Lpuis Figuier, ya taba fada a shekara 1888, cewar, samun wata hanya da zata hade kasar faransa da Ingila, wani babban abu ne da ake bukata domin bunkasa ci gaban zamani a yau. Ko da yake wannan batu ne da kusan shekaru 137 kafin shi Louis ya yi rubutu akai, masana ilimi da kuma marubuta da dama sunyi rubuce-rubuce a kai kwarai da gaske. A cewar su , kasar Ingila da kasar Faransa sune Kasashen da suke kann gaba a Duniya ta bangaren harkar sufuri da kuma karfin kasuwanci a Duniya. Duk da cewar nisan da ke tsakain iyakokin kasashen biyu bai wuce kilomita 34 ba , amma sai gashi harkar sufuri da kasuwanci na samun tarnaki kwarai da gaske.

To sakamakon iri tsaikon da kuma bata lokaci da jiragen-ruwa keyi a bangaren hada-hadar kasuwanci, ya sa dole aka fara tunanin samar da wata hanya da zata saukaka wannan al’amari. Wannan shine abin da ya haifar da tunanin gina hanya ta karkashin kasa, wadda kuma zata ratsa ta karkashin tsaunuka da kuma ta cikin teku, wannan hanya ita ce a yau ake kiranta da suna“The channel Tunnel’’ a Turance.

Daga yadda tarihin kirkirar fara wanna aiki ya nunar, andai fara tunanin yin wannan aiki tun a shekarar 1751 kuma anyi ta rubuce-rubuce akai da bada shwarwari da kwafa kwamitoci, da rubuta rahotanni da amincewa harzuwa 1986. To amma dai an kafa harsashin ginin wanna hanya ta karakashin kasa ne a ranar 1 ga watan Disamban 1990, aka kuma kammala a shekara 1994, kusan dai shekaru hudu cur, aka dau

An kiyast cewar wannan hanya dai ta lashe kudi wuri na gugar wuri har Dalar Amurka Miliyan $15,000:00 kokuma mu sukaka lissafin muce $ Biliyan 15.

Siffanta wannan hanya dai abin sai wanda ya gani, amma dai wannan aiki , aikine mai banmamaki da kuma ban taajibi kwarai da gaske. Domin ita dai wannan hanya , hanya ce da aka yi ta ta tagwayen hanyoyi guda uku, kuma kowaccensu kamar dai wani bututu ne aka gina shi a siffar wani sunduki-sunduki wanda ya ratsa ta karkashin kasa.

Hanyar tana da tsawon kilomita 51 wanda kuma kilomita 37 da rabi ya bi ta karkashin teku ne.Har’ila yau kuma zurfin inda hanyar take daga doron gasa , yakai kimanin kafa 150, amma duk da haka jirgin kasan da ake kira da suna Eurostar yana ratsa wannan haya ne a cikin minti 20 kacal.

Idan aka hade dukkanin tagwayen hanyoyin guda uku , za’a samu murabbain kilomita 153, wannan katafaren aiki kuwa Mutane a kalla 13,000 ne suka yi shi, wadanda suka hada da Injiniyoyi da kuma sauran ma’aikata, kuma an kiyasta cewar kasar da aka hako a yayin wannan aiki , tudunta ya nunka tudun Dalar giza ta birnin Alkahira da ke kasar Misra, har sau uku.

Wannan hanya dai mallakar dukkanin kasashen guda biyu ne , domin kuwa daga cikin kilomita 153 na tsawon tagwayen hanyoyin guda uku, kilomita 84 na yankin kasar Ingili ne,inda kuma kilomita 69 ya ke a bangaren kasar Faransa.

Dangane da aikin gyare-gyare , sai ince da kai , tun asali dai a wajen zana ita kanta wannan hanya, sai da aka gudanar da nazari akan zanen hanyoyi irin na karkashin kasa har sau 18 kafin a amince da fara wannan aiki, duk dai domin a tabbatar da ingancinsa kuma a kaucewa duk wani kuskure da kan iya faruwa ko dai a yayin da ake cikin gudanar da aikin ko kuma bayan kammala shi. Haka zalika kuma kamfanin da suka gina wannan hanya sai da suka bayar da garantee ko kuma ince tabbaci na shekara 120 wato ma’ana kamfanin zai gyara wannan hanya kyauta idan ta samu wani lahani kafin shekaru 120,hakan dai nanufin a takaice babu wani abu da zai iya haifar da wata illa ga wannan hanya ta lalace kota samu wani nakasu har tsawon shekaru120 sai dai fa ikon Rabbul izzati.