1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HAR ILA YAU JAMUS NA HUSKANTAR BARAZANAR KUNGIYOYIN ÝAN TA'ADDA NA KASA DA KASA - INJI OTTO SCHILLY.

YAHAYA AHMEDMay 17, 2004

Kungiyar leken asirin cikin gida ta nan Jamus, wato Bundesverfassungsschutz, ta ce har ila yau ana huskantar matsaloli a huskar tsaro, wadanda za a iya jibinta su da `yan tsageru da kuma `yan ta’adda daga ketare, da ke zaune a nan kasar. Ministan harkokin cikin gida, Otto Schilly ne ya bayyana hakan, a cikin rahotonsa na halin tsaron cikin gida, da ya gabatarwa maneman labarai a birnin Berlin.

https://p.dw.com/p/BvjV
Ministan harkokin cikin gidan tarayyar Jamus, Otto Schilly.
Ministan harkokin cikin gidan tarayyar Jamus, Otto Schilly.Hoto: AP

Jami’an kungiyar leken asirin cikin gida ta nan Jamus, wato Bundesverfassungsschutz, sun nanata cewa, halin tsaro na huskantar wata gagarumar barazana daga rukunan `yan tsageru a nan kasar, masu jibinta da kungiyoyin `yan ta’addan islama.

Bisa alkaluman Ofishin kididdiga ta tarayya dai, a karshen shekara ta 2003, kusan baki miliyan 7 da digo 3 ne ke zaune a nan Jamus, yawan musulmi daga cikinsu kuma ya kai miliyan 3. kungiyar leken asirin cikin gida ta Bundesverfassungsschutz, ta ce a halin yanzu wasu `yan tsiraru ne kawai ke cikin kungiyoyin `yan ta’addan. Gaba daya dai, yawansu zai kai dubu 31, a cikin kungiyoyi 24. Bugu da kari kuma, kungiyoyin Turkawa 6 ne ke da yawan mabiya.

Amma da yake gabatad da rahotonsa kan halin tsaron cikin gida a birnin Berlin, ministan harkokin cikin gida, Otto Schilly, ya ce magoya bayan kungiyoyin `yan tsagerun sun fi yawa a fakaice, fiye ma da yadda ake zato. A masallatai da cibiyoyin al’adun islama ne kuma kungiyoyin ke samun magoya bayansu, inji ministan. A galibi kuma, matasa ne suka fi nuna sha’awa ga shirye-shiryen wadannan kungiyoyin.

Ministan ya kuma yi garagdin cewa, irin hare-haren ta’addancin da ke aukuwa a wasu kasashe tare da asarar rayuka da dama, za su iya aukuwa a nan Jamus. Bisa cewarsa dai:-

"Har ila yau dai, mu ma a nan Jamus, muna huskantar barazana daban-daban. Babban kalubalen kuwa, yana da tushe ne a cikin kungiyoyin `yan ta’addan islama da kuma `yan tsageru."

Jami’an tsaro dai na ganin cewa, akwai `yan ta’adda da dama a nan kasar. Amma sun fake ne ba sa aikata wani danyen aiki, balle a farga da su. A ko yaushe kuma, za su iya tashi su yi aika-aikansu. Kasancewar rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr a Afghanistan ma kawai, zai iya zamo musu dalili na kai harin ta’addanci a kan wasu ababan bara a nan kasar.

Ban da dai barazanar ta’addancin da ake huskanta, rahoton da ministan harkokin cikin gida Otto Schilly ya gabatar, na kuma nuna cewa, tafarkin dimukradiyya ma na huskantar kalubale daga `yan tsagerun Jamus, masu bin ra’ayin rikau. Su ma wadannan rukunan, bai kamata a ki nuna damuwa da su ba. Za su iya ta da zaune tsaye idan sun sami damar yin haka, kamar dai yadda suka yi niyyar dasa bam a wani bikin dora tubalin ginin ibadan yahudawa a birnin Münich a shekarar bara, inji ministan. Mafi yawan wadannan `yan tsagerun dai, sun fi yin amfani ne da Internet wajen sadaswa.

Duk da sa musu ido da ake yi, `yan jam’iyyar nan ta NPD, wadda kotun kundin tsarin mulkin kasa ta hana haramtawa, suna ci gaba da harkokinsu. Sai dai yawansu ya dan ragu, daga dubu 6 da dari, zuwa dubu 5, a cikin shekarun bayan nan.