1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu tashi zaune tashi bata kare ba a kasar Srilanka

August 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bump

Sakataren Mdd, Mr Kofi Anan ya bayyana takaicin sa, a game da yadda tashe tashen hankula ke kara kazan ta a kasar Srilanka.

Bayanan na Mr Anan sun zo ne bayan wani hari na baya bayan da aka kai ramin hakar kwal, wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane 7, a hannu daya kuma da jikkata wasu 17.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Srilanka tace kungiyyar yan tawaye ta Timil Tigers ce ta kai wannan hari, wanda nufin sa shine a halaka jakadan kasar Pakistan, wanda motar sa na wucewa bom din ya tashi.

Wannan dai bom a cewar rahotanni ya tashi ne awowi kadan, bayan kungiyyar ta Timil Tigers ta zargi gwamnati da ragargaza gidan marayu, dake a yankin yan kungiyyar, wanda hakan yayi ajalin yara 61.

Tuni dai gwamnati ta musanta wannan zargi da cewa ta kai harin ne kann cibiyoyin karbar horo na yan kungiyyyar dake wannan yanki.