1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu ´yan Holland na adawa da kara fadada kungiyar tarayyar Turai

Mohammad Nasiru AwalJanuary 10, 2007

Daukacin ´yan kasar ta Holland na masu ra´ayin cewa yanzu lokaci yayi da ya kamata a shata kan iyakokin kungiyar EU.

https://p.dw.com/p/Btwi
Firaministan Holland Balkenende
Firaministan Holland BalkenendeHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka barkan mu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na MKT. Kimanin shekara daya da rabi da ta wuce al´umomin kasar NL da Faransa suka yi watsi da daftarin kundin tsarin mulkin KTT a wata kuri´ar raba gardama da suka kada. Fatali da kundin tsarin na Turai da kasashen biyu suka yi, ya janyo rikicin siyasa a wannan nahiya, inda dukkan harkoki na kungiyar EU suka gurgunce. Bayan kuri´ar raba gardamar FM NL ya ba da sanarwar shirya wata muhawwara game da nahiyar Turai a tsakanin al´umar kasar. To amma kawo yanzu shiru ka ke ji kamar an shuka dussa. A ma halin nan da ake ciki ´yan kasar ta NL ba sa son a tabo wata magana game da Turai. Hasali ma ´yan kasar ta Holland wadanda a da suka zama abin ko yi ga sauran nahiyar Turai, yanzu suna juyawa nahiyar baya. To wai shin menene dalili? To in kun biyo mu a hankali zaku ji karin bayani a cikin shirin na yau wanda ni MNA zan gabatar.

1. Atmo Marktstand:

Wata kasuwa kenan a kasar Holland. Tun kimanin shekaru 12 da suka wuce Bas van Vliet ke sayar da wandunan maza a wannan kasuwa da ake kiranta kasuwar Holland. Wannan kasuwa kuwa ita ce irinta mafi girma a nahiyar Turai baki daya kuma ta na a unguwar Schilderswijk dake The Hague, babban birnin Holland. A da leburori ne ke zaune a unguwar ta Schilderswijk amma yanzu ta zama wata matattarar baki ´yan ci-rani. A cikin shekarun baya aka yiwa unguwar kwaskwarima har ta zamo abin koyi. KTT mai hedkwata a birnin Brussels ta ba da euto miliyan 30 don gudanar da wannan aiki. Hatta shingen wayoyi da ya kewaye kasuwar ta Holland kungiyar EU ce ta ba da kudin kafa shi. To amma ´yan kadan ne daga cikin ´yan tireda a wannan kasuwa suka msan da haka. Hatta shi kan shi Bas sai a wannan karon ne ya samu wannan labari.

“Bana jin kungiyar EU ce ta ba da kudin kafa wannan shingen? Domin da kudin hayar rumfunan na kasuwar nan aka yi wannan aiki. Saboda haka ne hayar rumfa ke da tsada a wannan kasuwa.”

Bas mai shekaru 33 ba ya da wata cikakkiyar masaniya game da kungiyar EU. Kuma tun bayan watsi da kundin tsarin mulkin EU da ´yan Holland suka yi ba wani dan kasar da ya damu da batun kungiyar. A kuri´ar raba gardamar wadda aka gudanar kimanin sheakara daya da rabi da ta gabata, kashi 61 cikin 100 suka nuna rashin amincewar su da tsarin mulkin.

“Ya yi kyau abin da ´yan Holland suka yi. Domin Turai ta yi girma fiye da kima. Da kamata yayi tun da dadewa ta shata kan iyakokinta. In da za´a bi ta shawara ta, to ina ganin da kamata ya yi a daina amfani da takardun kudi na Euro, a sake dawo mana da kudin mu na Guilder. Ka ga har yanzu ina da takardar Guilder 10 a aljihu na. Shin haka bai ba ka sha´awa ba?”

Bayan kuri´ar raba gardamar, FM NL dan jam´iyar Chirtian democrat Balkenende ya ba da sanawar shirya wata babbar muhawwara kan nahiyar Turai a tsakanin jama´ar sa, to amma har yanzu ba wani abin da aka yi bisa wannan manufa. Domin ba wanda ke son ya jefa kansa cikin wani wadi na tsaka mai wuya a game da batun na Turai. A halin da ake ciki wakilan kasar ta NL a majalisar dokokin Turai da masu ilimin kimiyyar siyasa da kungiyoyin ma´aikata sun fusata akan abin da suka kira rashin wani katabus daga bangaren gwamnatin NL. Suka ce gwamnati a birnin The Hague ka iya kara rashin wani angizo a tsakanin kungiyar EU wanda a karshe zai iya janyo faduwarta kasa warwas. Wani mai rubuta sharhi yayi kashedin cewa idan aka ci-gaba a haka, to ka da a yi mamaki idan watan wata rana, Holland wadda ke tafiyar da kyakkyawar huldar kasuwanci da kasashen waje, ta wayi gari kowa ya juya mata baya.

A da kuwa akasin haka aka fuskanta, lokacin da Holland din ta abin koyi ga sauran kasashe Turai. A wancan lokaci ba ta saka ayar tambaya a game da harkokin hukumomin KTT, musamman dangane da fa´idar tafiyar da huldodin kasuwancin cikin sauki a tsakanin kasashen kungiyar. Ko da yake wasu na suka game da yawa yawan dogon turanci da kashe kudade barkatai a birnin Brussels, amma hakan bai karya karfin guiwar masu dokin ganin hadewar nahiyar Turai ba. Maimakon haka ´yan kasar ta Holland sun ci-gaba da taka rawa a matsayin abin koyi a tsakanin kasashen Turai.

Ad Verbrugge mai ilimin falsafar al´adu na birnin Amsterdam yayi bayani yana mai cewa.

“Mun yi imani cewa a wajen mu abubuwa da dama na tafiya daidai wa daida fiye da na sauran kasashen Turai. Mun yi kokarin daidaita manufofin mu da suka shafi alal misali mata masu zaman kansu, shan kwayoyi masu sa maye da dai sauransu. A takaice mun zama tamkar wasu ´yan mishan. Kasar mu kuwa ta kasance mai yada sakonni da kuma fata na alheri.”

Yanzu dai ´yan Holland sun gane cewar ba kowace kasa ce ke ba da muhimmanci ga manufofi tamkar na masu wa´azi ba. Maimakon haka ita da kanta ta na shan suka dangane da yin gaban kanta musamman saboda manufofin ta da suka shafi shan amfani da abubuwa masu sa maye. Hakazalika ´yan kasar ta Holland wadanda suka yi sna wajen harkar kasuwanci, sun yi ta fama da matsala wajen amfani da takardun kudi na Euro fiye da sauran kasashen Turai. Duk da cewa gudunmawar kudi da kasar ke ba wa kungiyar EU kadan ce, amma duk da haka ta na jin takaicin karo-karon da take bayarwar. A lokaci daya kuma ana kara nuna fargabar cewa a cikin kungiyar EU da take kara yin fadi, tasirin Holland a cikin kungiyar na raguwa yayin da na Brussels ke karuwa.

“Kamar yadda ya faru ne a cikin karni na 16 lokacin da muka nuna adawa da angizon daular Spaniya. A wancan zamani ma mun ji tsoron rashin wani iko da muke da shi. Bugu da kari a wancan zamani mun ga cewa ana mulkan mu daga ketare yayin da ake tatsar arzikin mu babu kakkautawa.”

Kisan gillan da aka yiwa dan siyasa mai matsanancin ra´ayin rikau Pim Fortun da wanda aka yiwa mai shirya fina-finai kuma sukar addinin Islama Theo Van Gogh sun jefa kasar ta Holland cikin wani rikici na rashin tantace asalin ´yan kasa. Har yanzu kuwa ba´a magance wannan rikici ba. Sannu a hankali kasar wadda a da ta kasance abin koyi, yanzu ta koma bayan madatsun ruwan ta ta ta kame bakinta ta yi shiru, inji Henk Kool shugaban sasahen tattalin arziki da zamantakewa na hukumar birnin The Hague.

“Nahiyar Turai ta wuce kaifin tunanin da yawa daga cikin ´yan kasar. Nahiyar ta yi musu girma da yawa. Hatta su kan su mazauna unguwar Schilderswik sun fi daukar kansu a matsayin ´yan wannan unguwa maimakon ´yan The Hague ko ´yan Holland.”