1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haramta kaciyar mata a Eritrea

April 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuOD

A kasar Eritrea, an haramta yiwa yara mata kaciya,tsohuwar alada da kungiyoyi agaji sukace yana barazana wa rayukan yara mata dake wannan kasa.Sanarwa da gwamnatin kasar ta tura ta hanyar yanar gizo gizo ,na nuni dacewa dukkan wanda aka samu da hannu a kokarin aiwatar ko kuma taimakawa aiwatar da kaciya akan wata ya mace ,zai fuskanci hukuncin zama a gidan kurkuku da kuma biyan kudaden diyya.Kasar ta Eritrea dai tayi fice a wannan alada.An kiyasta cewa kimanin yara mata million 140 ne aka aiwatar da wannan alada na shayi akansu,kuma hukumomin mdd sun bayyana cewa akalla a kowace shekara akan samu mata million 3 wadanda ke fuskantar barazanar wannan al’ada, asassa daban daban na duniya.