1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harbe harben rokoki a birnin Akaba na kasar Jordan

Yahouza sadissouAugust 19, 2005

An harba rokoki a rundunar sojojin ruwa ta Amurika dake gabar tashar jiragen ruwan Akaba na bahar Maliya a kasar Jordan

https://p.dw.com/p/BvaM

Wasu mutane da har yanzu ba a tantance ba, sun harba rokoki a yau juma´a ,ga sansanin rundunar sojojin ruwa ta Amurika, da ke tashar jiragen ruwan Akaba, ta kasar Jordan, a Bahar Maliya.

Saidai rokokin da su ka yi setin sojojin Amurika, ba basu cimma burin su ba, har ma sun yi sanadiyar mutuwar soja daya, na kasar Jordan, bayan da su ka durra a wurare daban daban.

Rokar farko ta fada bisa kan wani gidan assibiti ,sanan ta biyun a birnin Eilat na Israela, da ke gabar hauni ga kogin bahar maliya kussa da birnin Akaba.

Hukumomin kasar Jordan, sun fara bincike, domin gano wanda ke da alhakin kai wannan hare hare.

Alamomin farko, da a ka tattara ya zuwa yanzu, na zargin wasu mutane 2, na Iraki da kuma mutun daya na Syria, da a ka bayana cewa an gane su, wajejen da rokokin su ka tashi.

Saidai, tunni dakarun Abdallah Al Azam, wani reshe na kungiyar Alqaida a yankin sun, dau alhakin kai wannan hari.

Sanarwar da su ka bayana ta tabatar da cewa, rokokin sun bukaci hadasa mumunan barna ga rundunar Amurika, saidai su ka samu dan kuskure, wajen harba su.

Sanarwa ta kara da cewa, wannan soman tabi ne, ga saban yunkurin da dakarun su ka shiga na yakar Amurika a kasar Jordan, tare da zargin tshugaba Bush da mukaraban sa, da yada cin hanci da rashawa a dunia, da kuma kaka gida da dukiyoyi mallakar kasashen musulmi na dunia.

Haka zalika, sanarwar dakarun Al Azam, ta ce kamar yada ta fara girgiza shugaban Osni Mubarak na Misra, haka za ta bullo da wannan saban mataki, ga sarki Abdallah na Jordan, domin cilasta masa, yayi belin dukan yayan wanan wanan kungiya da duk wasu yan kishin addinin Islama, da ya ke tsare da su.

A halin da ke ciki, jami´an tsaro, sun yi zobe a yankin na birnin Akaba, wanda cibiya ce, ta fannin tattalin arzikin kasar Jordan.

Ita ma kasar Misra, ta tsawrara mattakan tsaro, a kogin Suez, mai hada bahar maliya, da mediteranne, domin riga kafi ga sulalawar yan yakin sa kan, a kasar Misra, mussamman, a daidai wannan lokaci, da ta kasar ta shiga yakin neman zabe.

Hukumomin Israela da na Amurika, sun bayana bada agaji, ga kasar Jordan, domin gano ainahin wanda ke da hannu a wannan dayen aiki.

Tunni Israela, da shiga shirin ko ta kwan, domin alamomi na nuna karuwar ire iren wannan hare hare.

A cen kuma zirin Gaza, a halin da ke ciki,jami´an tsaro sun yi nasara kwashe unguwani 17, daga jimmilar uguwannin 21 da yahudawa yan kaka gida su ka mamaye a zirin Gaza.

Haka zalika, sun kwashe matsugunai 2, na arewa ga kogin Jordan.

Sanarwar da jami´an yan sanda su ka fido ta bayana cewa, a lokacin da su ka fara kwasar yahudawan ,ranar litinin kimanin kashi 25 ne, kawai bisa dari, yan gani kashe ni su ka rage a zirin Gaza.

Unguwar Gadid da aka tasmaci, zata bada matukar matsala, ga sojojin Israela, itama a ranar yau juma´a tazama sakai.

Kakakin rundunar Israela, Janar Gai Tsur, da ke jagorantar wannan aiki, ya sanar cewa, a lokacin da su ka shiga yankin Gadid a sahiyar yau,mutane kimanin dari 2 ne, yan tsatsawran ra´ayi su ka tarda.

Wannan yan sai sun ga abunda ya turewa buzu nadi, sun yi matukar kalamomin batanci, ga yan sanda tare da zagin su uwa uba.

Bayan nasara farko, da su ka cimma, sojojin Israela,za su dakatar da aikin har ranar lahadi mai zuwa.