1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare a ƙasar Irak

May 13, 2007
https://p.dw.com/p/BuLb

To saidai a wani mataki na, a na magani kai na ƙaba, a ciga ba da tashe tashen hankulla a ƙasar Irak, yan ƙunar baƙin wake, sun kai sabin hare-hare, a arewan cin ƙasar a lahadin yau.

Mutane a ƙalla 35 su ka rasa rayuka,a yayin da wasu fiye da 100 su ka ji mummunan raunuka, a sakamakon wannan hari.

Ƙungiyar Al´Ƙa´ida, da Amurika ke zargi dakai wannan hare hare ba ji ba gani, ta bayyana capke wasu sojojin Amurika 3,wanda a halin yanzu ake nema ruwa jallo.

Rundunar sojojin Amurika a ƙasar Irak ta baza dakaru dubu 4, wanda ta ɗorawa yaunin gano wannan sojoji to ta halin ƙaƙa, kamar yadda Manjo Jannar, William Calwell kakakin shugaban rundunar, ya bayana:

„Mu na ci gaba da biciken wurin da aka boye wannansojoji guda 3, a game da haka mun tanadi dakaru dubu 4, don cimma buri.“