1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare sun hallaka mutane 29 a Kamaru

Mouhamadou Awal BalarabeOctober 11, 2015

Majiyoyi sun nunar da cewar mata ne suka kai wadannan hare-haren kunar bakin wake a wani gari ke kusa Mora na arewacin kasar ta Kamaru.

https://p.dw.com/p/1GmNY
Kamerun Soldaten Anti Boko Haram
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Chimtom

Wasu 'yan bindiga sun kai tagwayen hare-hare a garin Kangaleri da ke yankin kuryar arewacin Kamaru, inda suka yi nasarar hallaka mutane tara tare da jikata wasu 29. Wasu majiyoyi da ba su so a bayyana sunayensu ba sun bayyanawa kanfanin dillancin labaran Faransa cewar wasu mata biyu ne suka tarwatsa bama-bamai dake jikinsu a wannan gari da ke da tazarar kilo-mita 30 da Mora a safiyar wannan rana ta Lahadi.

Babu dai wata kungiya da ta dauki wadannan hare-hare, amma kuma ana dangantasu da wadanda tsagerun Boko Haram suka saba kaiwa a kasashe Kamaru da Chadi da Najeriya da kuma Nijar. Gwamnatin Kamaru ta yi amfani da wannan dama wajen jaddana aniyarta ta ganin bayan wannan kungiyar ta Boko Haram da ma dai ayyukan ta'addanci a kasar.

Fadar mulki ta Yaounde ta canza salon kamun ludayinta a yakin da take yi da Boko Haram tun bayan da hare-hare suka fara yawa a arewacin kasar. A yanzu dai baya ga rundunar sojojin kasa, ta fara amfani da jiragen yaki wajen kai wa 'ya'yan kungiyar hari a tungarsu.