1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare haren bam a Iraki

Hauwa Abubakar AjejeOctober 9, 2007

Yayinda ake shirye shiryen kammala azumi cikin wata mai tsarki da muke ciki,hare haren bam a kasar Iraki sai ci gaba sukeyi duk da ikrarin da rundunar sojin Amurka tayi cewa an samu raguwar hare haren cikin yan kwanakin nan.

https://p.dw.com/p/BtuQ
Hoto: AP

A yau din nan kadai hare haren kunar bakin wake kashi biyu sun halaka akalla mutane 22 a arewacin kasar a wani yunkuri na kashe wani babban jamiin yan sanda da wani shugaban kabila dan sunni da ke aiki da dakarun Amurka yakar Alqaeda.

Kungiyar ta Alqeda a Iraki dai ta lashi takobin inganta hare harenta a cikin wannan wata na Ramadan musamman akan jamian gwamnati da shugabanin kabilu da suka hada kai da dakarun Amurka.

Wadannan hare hare biyu na yau sun faru ne a Baiji ne dake da dauke da manyan matatun man fetur na kasar.

Yan sanda sunce daya daga cikin harin an kai ne kan wani masallaci daya kuma a gidan babban jamiin yan sanda kanar Saad Nufous inda ya samu rauni wani mataimakin babban jamiin yan sandan Mosul kuma ya rasa ransa cikin wani harin na dabam.

Wata majiyar yan sanda a Baiji sunce daya harin kuma an kai ne nufin kashe Hamad Jubouri dake majalisar yan sunni wadda ta kuduri aniyar yaki da yan Alqaeda.

Wannan majalisa tana kama da wata majalisa da aka kafa a lardin Ambar inda shehunan yan sunni suka hada kai da dakarun Amurka wajen fatattakar yan bindiga na Alqeada daga lardin,inda har shugaba Bush ya yabawa lardin da ingantuwar tsaro a matsayin wani misali abinda zai iya samuwa a sauran bangarori na kasar.

Lardin na Anbar dai ada shine mafi hatsari ga dakarun Amurka,amma aka samu tsaro tun bayanda shugabannin kabilu suka kafa yan banga a lardin.

Rundunar sojin Amurka tace a cikin yan kwanakin nan kungiyoyin kabilu sun kafa majalisu indavsuke kara karfi a yankuna kamar na Salahaddin inda manyan shugabannin kabilu har yanzu suke ci gaba da nuna goyon ga mariya Saddam Hussein.

Komandojin Amurka da gwamnatin Amurkan kanta sunce wani dauki day a hada da sojoji 30,000 na Amurka ya taimaka rage yawan mace mace nay an Iraki da dakarun Amurka a watan satumba.

Wannan dauki dai an shirya shi ne da nufin baiwa shugabbnin dake adawa da juna a Iraqin damar kaddamar da dokoki da nufin sasanta tsakanin yan sunni day an shia .

Rundunar sojin Amurka dai ta dora laifukan yawancin hare hare a Iraki kan kungiyar Alqeda kodayake ita kungiyar takan yi ikrarin kai wadannan hare hare.

Haren haren na yau dai sun abku kwana guda bayan akalla mutane 21 sun rasa rayukansu cikin harin bam na mota a jiya litinin.