1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Isra´ila a Palestinu

May 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuKu

Rundunar Isra´ila ta bayyana yin ƙofar rago ga zirin Gaza.

Sanarwar Gwamnatin Isra´ila, ta bayyana ɗaukar wannan mataki, da zumar garkuwa ga hare-haren yan yaƙin sunƙuru na Ƙungiyar Hamas.

Saidai duk da wannan mattakan tsaro, Hamas ta ce, ta harba rokoki 2, da sanhin sahiyar yau, a kan yankin Sderot mallakar Isra´ila.

Wani kakakin ƙungiyar Hamas, sami Abu Zuhri, ya ce Hamas ba zata daina cilla rokoki ba, har sai lokacin da bani yahudu, su ka dakatar da kai hare-hare a yankunan Palestinawa.

Tun daga ranar 16 ga watan da mu ke ciki, a ƙalla Palestinawa 40 su ka rasa rayuka, a sakamakon hare-haren kanuwa da wabi,ta sararin samaniya, da Isra´ila ta aiyyanar a zirin Gaza.

Wani saban hari rundunar Isra´ila ta kai a sahiyar yau, ya yi setin opishin ƙungiyar Hamas na zirin Gaza, amma ba hadasa asara rayuka ba.