1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Isra´ila a Zirin Gaza barazana ce ga zaman lafiya

January 19, 2008
https://p.dw.com/p/Cuo4

Masani kan haƙƙin bil Adama na Majalisar Ɗinkin Duniya a yankunan Palasdianwa John Dugard ya zargi Isra´ila da nuna hali irin na matsorata. Mista Dugard ya yi kira da a gurfanad da waɗanda suka kai hari kan ofisoshin gwamnati lokacin da ake wani bukin aure a kusa, gaban kotun dake shari´ar masu aikata laifukan yaƙi. A cikin wata sanarwa da ya bayar a birnin Geneva jami´in yayi tir da kisan da aka yiwa Palasdinawa fiye da 30 cikin makon nan a Zirin Gaza. Dugard ya ce Isra´ila ta karya ƙudurin Geneva da dokar kasa da kasa inda ta ki banbantawa tsakanin wuraren fara hula da na soji. Shi ma shugaban ƙungiyar ƙasashen Larabawa Amr Mussa ya yi Allah wadai da hare-haren sojin da Isra´ila ta kai Zirin Gaza da kuma rufe kan iyakokin yankin. Ya ce hakan zai yi mummunan tasiri a tattaunawar samar da zaman lafiya dake gudana yanzu tsakanin Isra´ila da Palasɗinawa.