1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren Isra’ila a zirin Gaza sun janyo mutuwar Falasɗinawa 10.

October 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bug6

Jiragen saman yaƙi Isra’ila sun kai hare-haren rokoki a birnin Gaza a cikin daren jiya, inda wasu ’yan ta kifen Falasɗinawa biyu da wani ɗan yaro suka sheƙa lahira nan take. Jami’an Hukumar Falasɗinawan sun ce jiragen sun harba rokokin ne a kan wani gida, wanda ake zaton na wani babban kwamandan ’yan ƙungiyar Hamas ne. Jami’an kiwon lafiyar Falasdinawan kuma sun ce an kawo mutane 7, waɗanda suka ji rauni sakamaokn harin, a asibiti, a cikinsu kuwa har da yara ƙanana. Mazauna Gazan dai sun ce a daura da yadda suka saba yi, a wannan karon dakarun Isra’ilan ba su umarni jama’a su fice daga gidajensu ba kafin su kai harin. A wani ɗaukin da suka kai jiya da safe ma, tankunan yakin Isra’ilan sun kutsa a kudancin ziirin na Gaza inda suka kara da ’yan ta kifen Falasɗinawa. A wannan ɗaukin dai jiragen saman Isra’ilan sun harba rokoki biyu, waɗanda suka halaka Falasɗinawa 6, a cikinsu har da wani ɗan yaro matashi mai shekaru 14 da haihuwa.