1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren kunar bakin wake a Kudancin Iraki

Salissou BoukariMay 1, 2016

Wasu tagwayen hare-hare da aka kai a wannan Lahadin a kasar Iraki, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 32 tare da jikkata wasu mutanen 75 a tsakiyar birnin Samaoua.

https://p.dw.com/p/1Ig6X
Irak Bagdad Selbstmordanschlag
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Ali

Bam na farko dai ya tashi ne kusa da cibiyar majalisar jihar, yayin da na biyu ya tashi kusa da inda motocin bus-bus ke tsaya wa kusa da inda na farkon ya tashi, inda ake ganin kungiyar ta IS dai ba ta saba kai irin wannan hari ba a wannan yanki.

Hakan na zuwa ne yayin da dubban masu zanga-zanga a yau Lahadi suka mamaye yankin nan da ke da babban tsaro na birnin Bagadaza inda manyan ma'aikatun gwamnati suke, bayan da a yammacin jiya suka mamaye majalisar dokokin kasar domin nuna kosawar su ga halayan 'yan siyasar kasar da suka kasa samun daidaito wajan kafa sabuwar gwamnatin mai muradin sauyi a kasa.