1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare haren taáddanci a kasar Iraqi

February 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6k

A kasar Iraqi an cigaba da fuskantar wasu tashe tashen hankula duk da dokar takaita zurga zurgar jamaá domin kwantar da tarzomar. Rahotanni sun baiyana cewa a kalla mutane shidda ne suka rasu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da wani dan kunar bakin wake ya tada nakiyar da yake dauke da ita a kusa da wani ofishin yan sanda a garin karbala. Harin ya auku ne jim kadan bayan da wasu yan bindiga dadi suka afkawa wani gida a kusa da Baquba dake arewa maso gabashin Bagadaza inda suka kashe mutane goma sha biyu. A waje huda kuma shugabannin yan sunni sun ce suna nazarin yiwuwar janye kauracewa shiga tattaunawar kafa sabuwar gwamnati da suka baiyana tun da farko bayan da P/M Iraqin Ibrahim Jaáfari ya yi musu alkawarin bada cikakkiyar kariya ga dukkanin masallatai na yan sunnin da kuma gyara wadanda aka lalata. Yan sunnin sun baiyana ficewa daga shawarwarin ne bayan harin bom din da aka kaiwa wani masallaci a birnin Samara da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.