1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren ta´adanci a ƙasar Yamal

July 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuHG

Hukumomin ƙasar Yamal sun bayana yaƙar ƙungiyar Alqa´ida bil haƙi da gaskiya, a sakamakon harin da su ka zarge ta, da kaiwa jiya litinin, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7 yan assulin ƙasar Spain.

A wani jawabi da ya gabatar, shugaban ƙasar Yamal, Ali Abdalah Saleh, ya ce, jami´an tsaro na da cikkakun rahhotani masu tabbatar da cewa, Alqa´ida ke da alhakin kai wannan mumuna hari, sannan ƙungiyar na cikin shirin kitsa wasu sabin hare-haren.

A game da haka, gwamnatin ta ɗauki matakai ƙwaƙƙwara na riga kafi , tare da binciko dukkan masu hannu a cikin harin na jiya.

Shugaba ƙasar Yamal, ya alkawarta bada tukuicin dalla dubu fiye da 80 ,ga duk wanda ya bada cikkaken bayyani a game da maɓuyar wannan yan ta´ada da su ke nema ruwa jallo.