1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren t'addanci a Somaliya

Abdourahamane HassaneApril 13, 2016

Mutane aƙalla guda uku aka ba da rahoton sun mutu a Somaliya kana wasu guda shida suka jikkata

https://p.dw.com/p/1IUhM
Somalia Anschlag Explosion in Baidoa
Hoto: Getty Images/AFP

Mutane sun mutu ne a cikin wasu hare-hare da wasu 'yan bindiga suka kai a kan wata kasuwa da ta saba cika maƙil da jama'a:

Wani babban jami'in tsaro ya ce 'yan bindigar sun jefa gurneti ne a cikin kasuwar da ke a garin Afgoye da ke da nisan kilomita 30 daga Mogadishu babban birnin ƙasar.Ko da shi ke ya zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin amma dai masu aiko da rahotanni na danganta harin da Kuniyar Al-Shebaab.