1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a makaranta a Amurka

Zainab A MohammedApril 17, 2007
https://p.dw.com/p/BvSt

Harin da wani dan bindiga dadi ya kai a harabar jamiar fasaha dake Amurka a jiya da safiya,ya haifar da rudani+ da tausayi tsakanin kasashen duniya ,tattare da dasa ayar tambaya adangane da matsalar hare haren yan bindiga dadi dake son zama ruwan dare a kasar ta Amurka.

Shugabannin kasashen duniya na cigaba da aikewa da sakonnin taaziyyarsu zuwa ga iyalan mutane 33 da suka gamu da ajalinsu a jamiar Virginia,wadanda suka hadar da dalibai da malamai da kuma shi kanshi dan bindiga dadin.

Prime ministan Austraslia John Howard yace wannan harin na Amurka ya tunatar masa da makamancinsa,inda wani ya buda wuta a garin Tasmania nan take ya kashe mutane 35 a 1996,wanda hakan ya tilasta gwamnatinsa sake nazarin batun mallakan bindigogi a bangaren jamaa.

Anan jamus ma wannan hadarin ya tunatarwa malamai da dalibai musamman na gaba da pramare,halin da kasar ta tsinciu kanta ciki lokacin da wani matashi ya harbe dalibai 16,shekaru 5 da suka gabata.

Wasu daga cikin dalibai da suka tsira da rayukansu daga harbin na jiya, a jamiar fasaha ta Blacksburg dake jihar Virginia,sun bayyana cewa dan bindiga dadin yayi kama da yan yankin Asia.,ayayinda jaridar Sun Times ta Chikago ta sanar dacewa yan sanda sun bayyana shi da kasancewa dan kasar sin ne kuma Dalibi ne mai shekaru 24 da haihuwa a makarantar, wanda ya shiga Amurka a watan Augustan daya gabata,wanada ya samu takardar izininsa daga birnin Shangai.

Kamaryadda Zeoma Teotoros daliba kuma yar kasar Habasha haififfiyar Amurkan ta shaidar.

A dangane da yadda wannan lamariya wakanh kuwa Zeoma tayi karin haske dacewa.

“Ya far ne da kashe wasu dalibai guda biyu,bayan kamar saoi biyu kuma ya sake shida wani aji inda dalibai ke daukan darasi,nan ya kulle kofar da sarka,kafin ya fara budewa daliban da malamai dake wurin wuta,ya kashe mutane da dama baya ga wadanda ya raunana,kafin ya juya ya jkashe kansa,don shima ya mutu”

To sai dai wannan dalibar ta bayyana cewa wannan lamari ya tsoratar da dukkan dalibai dake wannan makaranta domin basu san dalilinsa na yin wannan aika aika ba ,adangane da hakane suka tattara kayansu suka bar harabar makarantar.

Dan bindiga dadin dai ya kashe mutane 33 a jamiar fasaha ta Virgia dake amurkan a jiya da safe ,inda kawo yanzu baasan dalilansa ba.