1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HARI A TURKIYYA

ABUBAKAR D.MANINovember 20, 2003
https://p.dw.com/p/BvnX
Harin da aka kai a yau, a kasar Turkiyya akan ofoshin jakadanci na Britaniyya da kuma, bankin Britaniyya na HSBC, a Instanbul,ya dauki hankalin duniya.
Shugaban Amurka, George W. Bush, dake cikin ziyarar aiki, Britaniyya, ya bayyana cewar wannan harin, abun juyayi ne, kuma wani abu ne, wanda zai kara hada kawunan Amurka da Britaniyya da sauran kasahe, akan yakar wannan bala'in na yawaitar kai hare hare: Bush yace, za'a dage ganin an ci nasara akan yakar masu kai wadannan hare hare a ko ina suke a cikin duniya.
Bush dai tare da mai masaukinsa Prime Minista,Tony Blair na Britaniyya,sun ce, wannan harin na nuna, cewar, akwai bukatar yaki da ayyukan da suka kira na ta'addaci. Sun kuma ce, wannan ya nuna bukatar da ke akwai ta yakar Iraqi da kasashen nasu 2 tare da wasu kasashen suka taru suka aiwatar. Bush ya ce, manufar Amurka ta yakar Iraqi, akan hanya take, kuma tilas ne, ayi wannan yankin, kuma, babu wanda zai sauyawa Amurka manufofin ta, komin kai mata hare hare da akeyi ana kashe sojojin ta. Yace ba za'a dakata ba, har sai an kai gaci, a cikin manufofin Amurkar, a aikin da aka faran. Shi kuma Blai, cewa yayi, wannan kai harin na Turkiyya akan kaddarorin Britaniyya, ya nuna cewar lalle ana cikin halin yaki a yanzu, kuma kasar iraqi,, nanne babban fagen fama, a wanna yakin da ake ciki. Ya kara da cewar, duk hanyar bi, ta babu ji babu gani, za'a bita, a wannan karon battar yakin, har sai an ga bayan aikin da ya kira na ta'addanci, a ko ina, harda a Iraqi.Shi kuma sakataren harkokin waje na Britaniyyar,Jack Straw, cewa yayi, wannan kai harin,ya nuna yadda kungiyar Al-Qaeda da dangoginta, suke da kwakwaran shiri,na kai hare hare a ko ina cikin fadin duniyar nan. Prime Ministan Isra'ila, kuma, Areal Sharon, wanda yana cikin juyayin wancan harin, sai kuma ga wannan, yace kai hare hare, yanzu ya auri Turkiyya, wanda ya sanya, tilas a kara tashi tsaye akan yakar ayyukan da ya kira na ta'adancin da ba wai sun shafi Isra'ila kawai ba,ne, a'a sun shafi duk duniya ne. Shi kuma Ministan hulda da kasashen waje na Turkiyya, Abdulllah Gul,kira yakeyi akan kasashen Turai, da su sanya hannu, wajen yakar wannan aikin, wanda yake iya kaiwa ga ko wace kasa.
Kungiyar tarayyar Turai,ta bayyana cewar wannan kai harin da yayi sanadin rasa rayuka masu yawa, tare da jima mutane da dama, a Instanbul, a kasar Turkiyya, bai dace ba, komin irin manufar dake bayan kai harin. A cikin kasashen da suka bayyana rashin jin dadin wannan kai harin na Instanbul, a Turkiyya na yau din,wanda yayi sanadin mutuwar mutane da dama a ciki harda jakadan Britaniyya a Istanbul,Roger Short,harin da wata kungiya ta kasar Turkiyyar wadda ta ke kiran kanta,ta Jihadi, ta dauki alhakin kaiwa, akan kaddariorin Britaniyyar, akwai kasar Italiya, da Syriya, da Girka da Belgium da Denmark da dai sauran kasashen na duniya, tare da wasu kungiyoyi.