1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari kan asibiti a Yamen

Usman Shehu UsmanJanuary 10, 2016

Wani farmaki da aka kai a Saada babban birnin kasar Yamen ya fada kan asibitin kungiyar Likitocin bada agajin gaggawa na Doctors Without Boarders.

https://p.dw.com/p/1Hb3E
Jemen Saudi-arabischer Luftschlag in Sanaa
Hoto: Reuters/K. Abdullah

Harin wanda ya faru a yankin da 'yan tawaye suka fi karfi, ya yi sanadin rusa aksarin ginin asibitin. Dama can yankin da harin ya faru, ya sha samun hare-haren bama-bamai daga jiragen yakin Saudiyya. A cewar Raquel Ayora, daraktar gudanarwar ta kungiyar Doctors Without Boarders, asibitin sananne ne kuma duk masu yaki da juna babu wanda zai ce ba shi da masaniya inda suke bada agaji ga jama'a. A wannan harin dai mutane 10 suka jikkata, ko da yake ana kyautata zaton wadanda lamarin ya shafa za su karu. Wannan dai shi ne karo na uku a cikin watanni hudu da ake kai wa asibitocin kungiyar farmaki a kasar Yamen da yaki ya dai-daita. Kungiyar Doctors Without Boarders tana ci gaba da aikin bada agaji a jihohin takwas na kasar Yamen, duk kuwa da ficewar da kungiyoyin bada agaji daga Yamen ciki har da MDD, ta kwashe ma'aikatanta. Babu dai wanda ya dau alhakin harin da ya ruguza ginin asbitin kungiyar, amma sau da dama jiragen yakin Saudiyya suna yin luguden wuta a yankin, tun fara yin ruwan bama-bamai a kasar Yamen tun watanni 10 da suka gabata.