1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari kan ofishin jakadancin Amurka

Hauwa Abubakar AjejeSeptember 12, 2006

A yau din nan ne wasu yan bindiga suka kai hari kusa da ofishin jakadancin Amurka dake birnin Damascus na kasar Syria.

https://p.dw.com/p/BtyG
Hoto: AP

Wannan hari ya abku ne kwana guda bayan zagayowar shekaru 5 da kai harin ranar 11 ga watan satumba a Amurka.

Rahotanni daga kafofin yada labarai na Syria sunce,mutane 4 ne suka kai wannan hari na bam cikin kananan motoci guda 2 amma basu samu damar dana su ba,sai dai sunyi musayar wuta da jamian tsaro inda aka kashe dukkanin masu harin tare da kashe wani mai gadin ofishin.

Rahotannin sunce babu wani ba amurke daya samu rauni,amma wani jamiin diplomasiya na kasar Sin,wanda ofishinta ke kusa da na Amurkan ya samu rauni daga harbin bindiga na kan mai uwa da wabi da akayi.

Yanzu haka dai ministan harkokin wajen Syria Bassam Abdel Majid ya baiyana cewa zaa gudanar da bincike kan wannan hari,wanda har yanzu baa gano kungiyar data aikata shi ba.

A can birnin Washington,kakakin maaikatar harkokin wajen Amurka,Gonzalos Gallegos,ya tabbatar da kai wannan hari,sai dai shima a nashi bangare yace har yanzu baa tabbatar inda wadanda suka kai harin suka fito ba.

Hakazalika jamian kasar Syria basu tabbatar da ko suwa suka kai harin ba,sai dai a yan watanni da suka gabata jamian tsaro a Syria sun sha fafatawa da yan gwagwarmaya na islama,musamman a lokutan da suka je tsare su.

A watan yuni daya gabata, wasu yan gwagwarmaya 4,da wani mai gadi sun rasa rayukansu,a lokacinda jamian tsaron Syria suka ce sun rusa wani shiri na kai hari a kusa da gidan telebijin na kasar.

Dangantaka tsakanin Amurka da Syria dai tuni dama tayi tsami tuntuni,inda a watan fabrairu na 2005,Amurka ta janye jakadanta na Syria,tana mai baiyana abinda ta kira matukar bacin ranta game da kisan tsohon Firaministan Lebanon Rafik al Hariri.

Amurkan ta dora laifin wannan kisa akan Syria,ita kuma Syria ta karyata.

Hakazalika a baya bayan nan Amurka,ta ci gaba da sukan Syria lokacinda Israila ta kaddamar da yakin kwanaki 34 akan yan kungiyar Hezbollah,wadanda keda goyon bayan Syrian da kuma Iran.

Kasar ta Syria,wadda Amurka ke zargi da laifin taimakawa sojin sa kai a Iraqi da kuma goyon bayan Hezbollah da gwamnatin Hamas,ta dora laifin karuwar tashe tashen hankula a yankin,kan manufofin Amurka,musamman yaki a Iraqi da kuma goyon bayanta ga Israila.