1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Algeria

April 12, 2007
https://p.dw.com/p/BuNq

Shugabannin kasashen duniya da suka hadar da sakatare general na mdd Ban Ki-Moon sunyi Allah wada tagwayen hare haren kunar bakin wake da aka kai a fadar gwamnatin Algeria dake birnin Algiers a jiya,harin daya haddasa asaran rayuka akalla 33.Kungiyar masu tsattauran akidoji na addini kasar dai sun rataya alhakin kai wadannan hare hare.Daya daga cikin bomb din dai ya tashi ne daga cikin wata mota a kofar harabar prime ministan Algeria Abdelaziz Belkhsdem.Na biyun harin kuwa ya ritsa ne da ofishin yansanda dake gabashin birnin kasar Wadannan hare hare na jiyan dai sun kasance na farkon irinsu a kasar ta Algeria ,tun bayan kawo karshen yakin basasa a wannan kasa dake arewacin Afrika.