1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya halaka mutane 19 a birnin Bagadaza

May 20, 2006
https://p.dw.com/p/BuxX

Akalla mutane 19 sun rasu sannan kimanin 36 sun samu raunuka a wani harin bam da aka kai a gabashin birnin Bagadaza. Bam din ya fashe ne da sanyin safiyar yau asabar lokacin da wani gungun leburori ´yan shi´a suka hallara don nema aiki. Wannan harin dai ya zo ne sa´o´i kadan gabanin majalisar dokokin Iraqi ta fara shirin tabbatar da sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a ofis. Bayan watanni da dama ana fama da kika-kaka a fagen siyasa, a jiya juma´a shugabannin Iraqi suka amince da kafa sabuwar majalisar ministoci wadda ta kunshi manyan kabilu da kuma mabiya addinan kasar dabam-dabam. Ya zuwa yanzu kuwa ba´a bayyana sunayen wadanda za´a ba manyan mukamai na ministocin cikin gida da kuma na tsaro ba, amma rahotanni sun ce FM Nuri al-Maliki zai rike wadannan mukamai na wucin gadi.