1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HARIN BOM A ATHENS.

May 5, 2004

Jamiai tsaro na na binciken harin boma bomai daya ritsa da birnin athens a yau Laraba da safiya.

https://p.dw.com/p/Bvjx
Harin Bomb a ofishin Yansanda a birnin Athens.
Harin Bomb a ofishin Yansanda a birnin Athens.Hoto: AP/NASA

Kwanaki 100 gabannin fara gudanar da wasannin motsa jiki na Olimpics a birnin Athens,boma bomai 3 sun fashe yau a kofar ofishin yansanda dake babbar fadar kasar Girka,batu daya kawo damuwa damgane da harkokin tsaro,a wannan wasanni na motsa jiki mafi girma da ake shirin gudanarwa.

A Sydney,Australia cibiyar wasannina Olinpics,an bada umurni na gaggawa dangane da sake nazari kann matakan tsaro ,a dangane da shirye shiryen gudanar da wasannin motsa jiki na Athens,inda tuni ta sanar da tura ayarin jamiai domin tabbatar da kariy,koda yake tace bazata tsaya a hanya ba.

Gwamnatin kasar Girka tace babu alamun alakan wannan harin,da shirye shiryen wasannin na Olimpics.Prime minista kasar Costas Karamanlis ,ya fadawa taron manema labaru cewa,hadin kansu da kungiyar gamayyar turai ta EU,kungiyar tsaro ta NATO,da hukumomin Amurka,na dada tabbatar dacewa bazaa samu wata matsala ba dangane dangane da matakan tsaro wajen tabbatar dacewa an gudanar da wannan wasa har zuwa karshe.

Da farko dai jamian yansandan kasar sun sanar dacewa,akwai shaida dake danganta wata kungiyar tsageru,da wasu yan ta kife dake yawaita kai hare haren boma bomai a kewayen Athens.To sai dai tashin boma boman guda uku a kofar ofishin yansanda,na nuni da bukatar daukan tsauraran matakai kann harkokin tsaro,musamman a dai dai lokacin da ake shirye shirye na karshe,wajen gudanar da wannan gasa.

Harin Bomb din dai yazo ne,bayan gargadi da akayi ta wayan tangaraho,harin daya lalata ginin ofishin yansanda dake gunduwar,mai yawan alumma,kuma kusa da gine ginen hotel hotel ,da jamian wasannin Olinpics din zasu amfani dasu,wanda zai gudana tsakanin 13-29 ga watan Agusta,idan mai duka ya kaimu.

Rahotanni daga yankin dai da farko sun nuni dacewa wani jamiin yansanda ya samu raunuka sakamakon wannan harin,amma majiyar yansandan tace babu wanda ya samu rauni.Tuni dai jamian tsaro suka duka kain da nain wajen tabbatar da nasaran gudanar da wasannin,wanda zai kasance na farkon irinsa,tun bayan harin kunar bakin waken 11 ga watan satumban shekara ta 2001 wa Amurka.

Mai magana da yawun komitin dake daukan nauyin wasannin,Gissele Davis,tace suna tuntuban hukumomin kasar Girka,wadanda kuma ke basu cikakken hadin kai da suke bukata,kana babu alamun wata dangantaka tsakanin harin Bomb din da shirye shiryen Olimpics.

Shi kuwa prime ministan Australia John Howard ,ya sanar da tura ayarin jamian tsaro domin kare lafiyan yan wasan kasar da zasu je wannan gasa,musamman ma idan aka cigaba da fuskantar barazana makamancin tashin boma boman na yau.Sai dai dai yace ana bukatar lokaci na binciken wannan harin,wanda hukumomin Girka suka danganta da kungiyar tsageru na cikin gida,a maimakon na yan taaddan kasa da kasa.Kasashen Amurka na Da Britania,na shirin tura jamian tsaro da zasu kare yan wasannin su a Athens.Shi kuwa shugaban komitin Olimpics na Australia,John Coates cewa yayi babu gudu babu ja da baya dangane da gudanar da wasannin a ranakku da aka ajiye.Shima ministan harkokin wajen kasar Alexander Downer,wasi yayi da kowace irin bazana daka iya bullowa kamar na yau.yace duk dacewa babu alamun dangantaka tsakanin harin na yau da Olimpics,akwai bukatar sake nazari kann ire iren wannan barazana,tare da tattauna yadda zaa shawo kansu.

Rahotanni daga Girkan dai na nuni dacewa,zaa kashe Euro billion daya kann harkokin tsaro,ayayinda sama da jamian tsaro dubu 50 ne zasu kasance a Athens,daura da tallafi da hukumomi suka nema na jiragen sintiri a sararin samaniya,da cikin ruwa ,tare kuma da shirin kariya na musamman daga makamai masu guba,daga kungiyar tsaro ta Nato.