1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HARIN BOMB A IRAQI

JAMILU SANIJanuary 28, 2004
https://p.dw.com/p/BvmG
A kasar Iraqi yau ne wani dan kunar bakin wake ya tashi bomb din da aka dasa cikin wata mota mai nauyin kg 180 a wajen wani hotel dake birnin Bagadaza,wanan hali dai yayi sanadiyar yan asalin kasar ta Iraqi biyu da raunata wasu da dama yayin da wanan harin bomb ya lalata gaban ginen wanan hotel din mai hawa uku dake birnin na Bagadaza.

Majiyar yan sandan Iraqi ta baiyana cewa harin bomb din da aka kai wajen hotel din Shaheen,dake zaman mazaunin ministan kwadagon Iraqi da kuma wasu baki yan kasahen waje,yayi sanadiyar mutuwar mutane hudu,to sai dai kuma dogarin ministan kwadagon na Iraqi ya baiyana cewa wanan hari bai shafi ministan kwadagon na Iraqi ba.

Tun da farko dai sai da mai magana da yawun sojin Amurka a Iraqi,ya baiyana cewa mutane uku suka rasa rayukan su sakamakon wanan harin bomb,to amman kuma daga baya sai aka ce dreban motar da aka kai wanan hari shima ya rigamu gidan gaskiya.

Mai magana da yawun sojin na Amurka ya kara da cewa motar da aka yi amfanin da ita wajen kai wanan harin bomb a wajen hotel din na Shaheen na birnin Bagadaza nada launin fari da kuma ratsin ja,tare kuma wani tambari dake nuna cewa wanan motar malakar kungiyar bada agaji ce ta Red Cresent da ake amfani da ita wajen daukar marasa lafiya,to amman kuma aka yi amfanin da wadanan dabaru wajen kai wanan harin bomb a birnin na Bagadaza.

Wanan harin bomb din dai ya zo ne bayan kwana daya da wani munmunan harin bomb din da aka kai a kasar ta Iraqi,wanda kuma yayi sanadiyar mnutuwar sojin Amurka shida da kuma wasu jami'ai biyu na gidan talbijin din CNN dake Iraqi.

A sabili da haka ne baban sakataren majalisar dikin duniya Kofi Anann ya baiyana cewa zasu iya aika jami'an majalisar dikin duniya don su yi nazari game da shirye shiryen da aka sanya a gaba na zabe a Iraqi,amman fa sai an sami tabaci na inagantuwar harkokin tsaro a kasar ta Iraqi.

Majiyar data fito daga majalisar dinkin duniya ta baiyana cewa tun a jiya talata wasu jami'an majalisar dikin duniya suka fara issa kasar Iraqi,don yin nazari game da inagantuwar harkokin tsaro a kasar tun ma kafin a ce majalisar ta dinkin duniya ta dauki matakan mayar da aiyukan jami'anta a kasar ta Iraqi. Mai tsaron lafiyar ministan kwadagon Iraqi ya baiyana cewa suna cikin aiki wanan mota ta dumfaro su,koda yake sun bude mata wuta amman kuma bata iya tsayawa ba.

A yau laraba ne dai ake sa ran ministan kwadagon Amurka Elaine Chao zai fara gudanar da ziyarar aiki a birnin Bagadaza. A nasa bangaren shugaban musulmi yan Shi ite Ayatullah Ali al-Sistani cewa yayi,kamata yayi Amurka ta baiwa yan asalin kasar ta Iraqi damar shugabanin su da kann su ba wai Amurkan ta nada musu yan korenta ba.

A ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa ne dai Amurka ta shirya cewa za'a mika mulki ga yan asalin Iraqi,to amman kuma da wuya hakan ya tabata a sabili da matsaloli da ake fuskanta na tabas din harkokin tsaro a kasar ta Iraqi. +