1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Isra'ila kan jami' an agaji na shan suka a duniya

Abdullahi Tanko BalaMay 31, 2010

ƙasashen duniya na yin Allah wadai da harin da ya salwantar da rayuka 19 da dakarun Isra'ila suka aiwatar kan tawagar da ke jigilar kayan agaji i zuwa zirin gaza na Palesɗinu.

https://p.dw.com/p/Ndto
Zanga-zangar adawa da manufofin Isra'ila a GazaHoto: AP

Aƙalla jami' an na ƙasa da ƙasa19 aka tabbatar da cewa sun rigamu gidan gaskiya, yayin da wasu ƙarin 30 ke cikin halin rai kwakwai mati kwakwai sa' o' i ƙalilan bayan buɗe ma jiragen ruwan da suka nufi zirin gaza da dakarun na Isra' ila suka yi. Tawagar dai ta sha alwashin kai wa mazauna zirin gaza na Palesɗinu ɗauki da suke bukata ne, kama daga na abinci har i zuwa magunguna da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum. Sai dai dai dakarun na Isra'ila da dama ke cikin shirn suka buɗe ma ɗaya daga cikin jiragen agajin da suka taso daga nahiyar Turai wuta bayan da suka yi burus da kashedin sojojin na Isra' ila.

Gaza Angriff Israel
Tankar yaƙin Isra'ilaHoto: AP

Galibin kafafen watsa labarai na duniya sun watsa hotuna da kuma rahotannin da ke nuni da cewa dakarun na isara'ila da ma suna cikin shirin ko ta kwana. Hasali ma dai, sun yi amfani da jiragen masu saukar angulu da kuma manyan makaman yaƙi wajen ja ma tawagar da ke ɗauke da kayan agajin birki. sai dai kakakin rundunar sojojin  Isra' ila, wato Avi Benayahu ya danganta wannan mataki da martani ga takalar Isra'ila da wasu ɓangarori duniya ke yi.

Tuni dai Turkiya ta bai wa jakadan ta da ke Tel-Aviv umurnin tattare nasa ya nasa ya fice daga ƙasar Isra' ila domin nuna ɓatsin ranta. 'Yan ƙasar na daga cikin waɗanda suka fi jikata a wannan farmakin. Papa Roma Benedikt na 16 shi ma ya shiga sahun shugabannin duuniya da ke Allah wadai da abin da ya kira amfani da tsinin bindiga da Isra' ila ta yi wajen ja ma tawagar Birki. ƙungiyar gamayyar Turai anata ɓangaren ta tanadi wani taron gaggawa na jakadun ƙasashe mebobinta a wannan yammaci domin cimma matsaya guda. Shugaba Mahmoud Abbas ya danganta wannan harin da rashin imani.

Israel Angriff in Gaza Ministerpräsident Ismail Hanija und Präsident Mahmoud Abbas
Mahmud Abbas na nuna baccin raiHoto: AP

Uwar gijiyar ta Isra'ila wato Amirka, da kuma sauran ƙasashen da ke ɗasawa da Isra'ilan ciki kuwa har da Birtaniya, alhini kawai suka nuna game da salwantar rayuka da aka fiskanta bayan farmaki na sojojin Isra' ila. Alhali ana kyatata zaton cewa shugaban ƙungiyar musulmi ta Isra'ilan na daga cikin waɗanda suke cikin hali ni 'yasu sakamokon mummunan rauni da ya samu a harin na dakarun Isra'ila.

 Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou