Harin kunar bakin wake a kasar Pakistan
November 15, 2005Talla
Hukumomin yan sanda a kasar Pakistan sun sanar da aukuwar fashewar bom a wani dakin cin abinci a birnin karachi wanda ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane shida da jikata wasu da dama. Baturen yan sanda na birnin Karachi Mushtaq Shah ya baiyana fashewar bom din wanda aka dasa a cikin wata yar karamar mota da cewa hari ne na taáddanci wanda aka kitsa domin haddasa mummunan barna. Babu wata kungiya da ta baiyana daukar alhakin kai wannan harin.