1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake a Morocco

March 12, 2007
https://p.dw.com/p/BuPo

Mahukuntan ´kasar Morocco sunce wani dan kunar bakin wake ya tada bam din dake jikinsa a wani gidan internet a birnin Kasablanka a daren jiya,yana mai halaka kansa tare da raunata wasu mutane 3,yan sanda sunce suna gudanar da bincike akai.

Bam din ya tashi ne a lardin Sidi Moumen mazaunin wasu yan kunar bakin wake su 13 da suka halaka kawunansu tare da wasu 32 a 2003.