1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kunar bakin wake ya halaka mutane a Kamaru

Yusuf BalaSeptember 13, 2015

Mijinyawa Bakari gwamnan Arewa mai Nisa ya ce wasu mayakan sakai uku ne suka kai harin a safiyar Lahadin nan, harin kuma da ya raunata wasu 18 da tuni aka garzaya da su asibitin Mora.

https://p.dw.com/p/1GVqK
Kamerun Anschlag in Maroua
Jami'ai da ke aikin tallafiHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Mahukunta a kasar Kamaru sun bayyana cewa wani harin kunar bakin wake ya yi sanadin halaka mutane bakwai a garin Kolofota inda mayakan Boko Haram masu sansani a Najeriya ke ci gaba da kai hari irin na sari ka noke.

Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan da kwamandan dakarun hadin gwiwa na kasashe biyar daga Najeriya ya kai ziyara sansanin soja a garin Mora lokacin da ya je shirin girka dakaru 2,500 a arewacin na kasar ta Kamaru.

Kungiyar mayakan Boko Haram na kara kai hare-hare a makwabtan kasar ta Najeriya kamar su Chadi da Kamaru da Nijar a cikin wannan shekara.

Kimanin kauyika biyar ne mayakan na Boko Haram suka matsa wa lamba a kasar ta Kamaru inda suke zuwa sace-sace da kona gidaje.