1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kyamar baki a gabashin Jamus

April 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1h

Wani Bajamushe dan shekaru 37 mai asali da nahiyar Afirka na kwance rai hannun Allah sakamakon mummunan raunin da ya samu a wani hari na nuna wariyar launin fata da aka kai masa a birnin Potsdam dake gabashin kasar ta Jamus. ´Yan sanda a birnin sun ce mutumin wanda ke da launin fata baki-baki, an kai masa harin ne da sanyin safiyar jiya lahadi a tsakiyar birnin. Kuma yanzu haka yana kwance asibiti rai kwakwai mutu kwakwai. Hukumomi a birnin sun ce suna neman wasu mutane biyu bisa zargin yunkurin yin kisan kai.