1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun rasa ransu a Najeriya

Muntaqa Ahiwa / LMJNovember 18, 2015

A Najeriya sama da mutane 30 ne akasarinsu kananan yara ake fargabar sun mutu bayan wani dan kunar-bakin-wake ya tayar da bom din da ke jikinsa.

https://p.dw.com/p/1H7Zf
Hare-haren ta'addanci a birnin Yola na jihar Adamawan Najeriya
Hare-haren ta'addanci a birnin Yola na jihar Adamawan NajeriyaHoto: picture alliance/AA/M. Elshamy

Rahotanni sun nunar da cewa dan kunar bakin waken ya tayar da bom din ne a tashar Tipa da ke hanyar bayan gari a Jimeta Yola da ke jihar Adamawa a daren jiya. Ana fargabar cewa akwai yiwuwar harin ya yi munin gaske, kasancewar wajen da lamarin ya faru na kusa ne da kasuwar dabbobi da kayan gwari da kuma Masallaci. Wakilinmu na Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa Muntaqa Ahiwa, ya ruwaito cewa, harin ya afku ne a dai-dai lokacin da ake hada-hadar bayan Sallar Magariba. Wani shaidan gani da ido ya shaidawa wakilin namu cewa yaga gawarwakin mutane da dama mafi yawansu yara da ke yin talla a wannan tasha. Ko a watan Oktoban da ya gabata ma dai sai da wani harin na bom ya hallaka mutane da dama a wani Masallacin juma'a a birnin na Jimeta.