1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin gudanawar gwamnatin Amirka sun tsaya ciki

January 20, 2018

Harkokin gudanar na gwamnatin da ta fi kowacce karfi a duniya wato Amirka sun tsaya cik a wannan Asabar, bayan gaza samun daidaito tsakanin shugaba Trump da kuma 'yan majalisar kasar na jam'iyyar Democrat.

https://p.dw.com/p/2rDPn
US-Präsident Donald Trump
Shugaba Donald Trump na AmirkaHoto: picture-alliance/abaca/O. Douliery

Bangarorin jagorancin Amirkar sun gaza cimma matsaya a kan samar da kudaden tafiyar da gwamnati da kuma matsalar bakin haure, abin da ya fito da bambancin da ke a Amirka a yanzu. Lamarin ya tilasta rufe wasu harkokin da ake ganin ba su da muhimmanci, kuma babu wani da ya san halin da ake ciki dangane da musayar yawun kyautata lamarin.

Gardamar kuwa na faruwa ne shekara guda cif da kama madafun iko da shugaba Donald Trump ya yi. 

Wannan ne dai karo na farko tun bayan irinsa da aka gani cikin watan Oktobar shekarar 2013, inda harkokin gudanar da Amirka suka yi tsayuwar kwanaki 16 cur.