1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

290410 Portugal Finanzen

April 29, 2010

Gwamnatin ƙasar Portugal ta ƙuduri aniyar fara aiwatar da shirin yiwa tattalin arzikinta kwaskwarima gabanin lokacin da aka shirya yi da farko.

https://p.dw.com/p/NAKi
Tsabar kuɗin EuroHoto: picture-alliance/dpa

Wannan matakin da gwamnatin ta Portugal ta ɗauka yana matsayin martani ga rage matsayin ƙasar dangane da ƙarfin biyan basussukan dake kanta. Yanzu haka dai gwamnati da ma 'yan adawa sun ce za su haɗa kai domin magance wannan matsala.

Duk da cewa ba za a iya yin watsi da dukkan banbance banbancen ra'ayin siyasa ba, amma abin da aka sa a gaba yanzu shi ne a gudu tare a tsira tare domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar ta Portugal. An jiyo waɗannan kalaman ne daga Carlos Coelho shugaban babbar jam'iyar adawa ta masu ra'ayin mazan jiya, lokacin da yake jawabi kan rikicin kuɗin. Jim kaɗan bayan haka Firaministan Portugal Jose Socrates ɗan jam'iyar Socialist ya ce gwamnatinsa za ta haɗa kai da jam'iyar PSD.

"Gwamnati da PSD dake matsayin jam'iyar adawa mafi girma sun amince da su yi aiki tare. Abin da muka sa a gaba shi ne mu samu amsa ga hasashe maras hujja da 'yan baranda suka yi. Sai kuma maido da yarda game da hannayen jarin gwamnatin Portugal."

Firaministan ya ci-gaba da cewa da cewa Portugal za ta sauke nauyin dake kanta, yana mai cewa za su haɗa hannu da hannaye domin ƙarfafa yardar kasuwannin hada-hadar kuɗi ga tattalin arzikin ƙasar.

Tun wasu watanni da suka gabata Portugal ta gabatar da tsare tsaren tsuke bakin aljihun gwamnati da suka ƙunshi wasu matakai dake shan suka. Ciki har da ƙayyade albashin ma'aikatun hukuma da rage yawan kuɗin fansho. To sai kuma gashi ana shirin rage yawan kuɗaɗen tallafawa jama'a kamar tallafin da ake bawa marasa aikin yi. Bugu da ƙari kuma yanzu ba zato ba tsammani gwamnati ta ƙuduri aniyar aiwatar da shirin tsimi da tanadi na gaba da wa'adi kamar yadda Firaminista Jose Socrates ya nunar.

"Na yiwa Carlos Coelho bayani dalla dalla cewa tun a wannan shekara gwamnati za ta fara aiwatar da matakan yiwa tattalin arzikin ƙasa kwaskwarima, amma ba a shekara mai zuwa kamar yadda aka tsara tun farko ba."

Daga cikin matakan har da sabon tsarin haraji ga masu albashi mafi tsoka, da harajin zirga-zirgar motoci akan manyan tituna sai kuma haraji akan riba a kasuwannin hada-hadar hannayen jari. Sannan za a ɗage aikace aikacen gwamnati da ba su da muhimmanci sosai.

A kuma halin da ake ciki hukumar dake ƙimanta ƙarfin tattalin arzikin ƙasashe wato Standard and Poor's wadda a ranar Talata ta rage ƙarfin Portugal game da biyan bashi wanda haka ya ƙara jefa ƙasashen dake amfani da takardun kuɗi na Euro cikin hali na tsaka mai wuya, yanzu haka ta rage ƙarfin ƙasar Spain a fannin tattalin arziki.

Mawallafi: Reinhard Spiegelhauer / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar