1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

140410 Nigeria Regierung

April 14, 2010

Duk da cewar kusan rabin shekara kenan shugaban Nigeria ke fama da jinya, harkokin mulkin na cigaba da gudana

https://p.dw.com/p/MwRg
Umaru Musa Yar'AduaHoto: AP

Tsawon lokacin da shugaban Tarayyar Nigeria Umaru Musa 'Yar adua ya dauka yana fama da rashin lafiya a 'yan watanni da suka gabata,ya haifar da  mahawara a nan Jamus kamar sauran ƙasashen dangane da batun  shugabanci a fadar gwamnatin dake Abuja.Musamman bisa la'akari da irin rigingimun da ƙasar ta tsinci kanta. Sai dai kwararrun na ganin cewar hakan bai haifar da  illa sosai a wannan kasa dake da mafi yawan al'umma a Afrika ba.

Ɗan Jarida kuma tsohon Edita a gidan Radiyon Dw Heinrich Bergstresser yana ganin cewar, ba za'ayi la'akari da abunda ya faru cikin 'yan watanni da suka gabata a Nigeriyar, a matsayin rigingimu ko tashin hankali ba. A cewar bergstresser, manyan 'yan siyasar kasar, akarkashin jagorancin  gwamnoni jihohinta 36 na , sun dauki matakan shawo kan matsalar ba tare da la'akari da banbancin siyasa, addini ko  kabilanci ba.

Nigeria Jonathan Goodluck
Goodluck JonathanHoto: AP

"Wannan gagarumin mataki ne, musamman a ɓangaren gwamnonin Nigeriyar da sukayi kaurin suna da rashin shugabanci na gari, sun cimma tsallake banbance banbance dake tsakaninsu, tare da tursasawa majalisar kasar wajen samar da ƙasar gwamnati mai Alqibla.Muna  da mataimakin shugaban kasa, wanda zai iya maye wannan gurbi. Abun da yan bamu dashi, wanda kuma ya zamanto wajibi a samar da mafita shine, mataimakin shugaban kasar bashi da karfin iko, ku bashi wannan damar, kuma sun cimma nasarar hakan"

 Jaiye Doherty  daga ƙungiyar kasuwancin Nigeria da Jamus dake Lagos, ya yabawa lamura da suka wakana a Nigeriyar a  'yan watanni da suka gabata. Yace abokan kasuwanci su Jamusawa sun sha tambayar shin me ke faruwa a Nigeria? Amma a yanzu kusan za a iya cewar hakan ya zama tarihi...

"Ba na ganin wanna yanayi ya haifar da illa kan dangantakar kasuwancin Nigeria da Jamus. Domin ya daɗa tabbatarwa da Jamusawa cewar, 'Yan Nigeria suna da tsarin mulki wanda su ke bi"

 Klaus Pähler na cibiyar raya al'adu ta Konrad -Adenauer shima yayi amana da hakan. Cibiyar dake da alakar kusantaka da jami'yyar Christian Demokrat ta nan Jamus dai, ta sha gudanar da taron karawa juna sani da amafani da kafofin yada labarun kasar, wajen gudanar da shiri na musamman kan  tsarin mulkin demokradiyya.

Öl Industrie Afrika Arbeiter auf einer Öl Plattform in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/dpaweb

A 'yan watanni masu gabatowa kafin gudanar da zaɓe dai, Pähler yayi imanin cewar zai gudana bisa tsari, idan aka kwatanta da yadda ya hangi lamarin a 'yan watannin baya.

 A cewarsa, duk da cewar mukaddashin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ba zai yi takara a zaɓen ba, ya zamanto wajibi ya tabbatar da yiwa dokar zaɓen Nigeriyar  gagarumin gyaran fuska...

" Yace alal misali, idan dokar zaɓen ta kasance kamar haka; idan yayi gyaran dokar zaɓen, kana ya samar mata shugaba mai inganci, zai iya kasancewa kyakkyawan misali ta hanyar da ta dace"

 Pähler dai yayi imanin cewar bayan garon bawul wa majalisar ministoci, a yanzu haka Jonathan yana jin daɗin tafiyar da lamuransa da sabbin ministocin da shi da kansa  ya nada, domin babu fargabar zagon ƙasa daga ko wane ɓangare. Sai dai babban kalubale  da har yanzu  gwamnatin Jonathan ke fuskanata, shine rikicin yankin Niger Delta, yankin da shi mukaddashin shugaban Nigeriyar ya fito. Acewar Pähler....

" Abun da watakila ya rigaya ya sani shine muhimmancin waɗannan matsaloli. Yana da matukar muhimmanci daya sa fifiko akai, domin rashin samun nasara  dangane da rikicin  yankin Niger Delta, na nufin har yanzu  da sauran rina a kaba, dangane da  kyakkyawar makoma a Nigeria".

 Kwararru kan Nigeriyar dai sun soki yadda jamus bata damuwa da harkokin siyasar ta Nigeria. A cewarsu da yawan al'umominta miliyan 150, da ɗunbin albarkatu da Allah ya hore mata, baya ga muhimmancinta a yankin, kawance da Nigeriyar yana da alfanu a ɓangaren Jamus. Dangane da hakane ya zamanto wajibi, Jamus ta kara inganta dangantaka da ita.

.

Mawallafa:Thomas Mösch/Zainab Mohammed Edita:Yahouza Sadissou