1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa a Guinea sun fara dai dai ta

February 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuR4

Shugaban kasar Guinea, Lansana Conte ya nada tsohon jami´in diplomasiyya, wato Lansana Kouyate, a matsayin sabon faraministan kasar.

Hakan dai ya biyo bayan matsin lamba ne daya fuskanta daga kungiyoyin kwadago na kasar, na sauya faraministan na da.

Kungiyoyin kwadagon kasar dai sun zargi tsohon faraministan na da ne da zama dan koron Mr Conte.

Mr Kouyate dan shekaru 56 ya dare sabon mukamin faraministan kasar ne, bayan da aka zabo shi daga cikin mutae guda hudu da kungiyoyin kwadagon kasar suka gabatar.

Yajin aikin sai baba ta ganin da kungiyoyin kwadagon suka gabatar ya haifar da asarar rayuka sama da dari, sakamakon arangama da aka dinga yi a tsakanin su da jami´an tsaro.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa yajin aikin ya biyo bayan irin kunci na rayuwa ne da da yawa daga cikin al´ummar kasar ta Guinea ke ciki ne.