1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa a Pakistan

November 14, 2007
https://p.dw.com/p/CDnN

Jami´an tsaron Palasɗinawa na ɓangaren shugaba Mahmud Abbas, sun cafke tsagerun ƙungiyyar Hamas 22.An cafke tsagerun ne a wani sintiri da Jami´an tsaron suka gudanarne, a kusa da arewacin garin Nablus.Rahotanni sun nunar da cewa jami´an tsaron sun shafe awowi kusan shidda suna gudanar da wannan sintiri.Ɗaukar matakin, yazo ne a dai dai lokacin da Faraministan yankin, wato Salam Fayyad da kuma Jami´in diplomasiyyar Amirka a Jarusalem, Mr Jacob Wallace, ke shirin kai ziyara ne izuwa yankin na Nablus. Yaƙi da ayyukan tsageru a yankin dai na ɗaya daga cikin sharuddan, dawo da daftarin zaman lafiyar nan na yankin na gabas ta tsakiya cikin hayyacinsa ne.A watanni kaɗan masu zuwa ne ake sa ran gudanar da taron kolin cimma zaman lafiya,a tsakanin ɓangarorin biyu ne, a jihar Maryland dake Amirka