1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa a Uganda sun tsananta

January 5, 2006
https://p.dw.com/p/BvDe

Mahukuntan kasar Uganda na yunkurin sake cafke madugun adawa na kasar , wato Kizza Besigye, bayan umarnin sakin sa da wata babbar kotun kasar tayi kwanaki kadan da suka gabata.

A cikin wata takarda da babban atoni na kasar , Khiddu Makubuya ya aikewa kotun kolin kasar, ya tabbatar da cewa akwai kura kurai a dalilan da alkalin babbar kotun ya bayar ,wajen sakin shugaban adawar kasar, a don haka akwai bukatar kara cafke shi.

A dai ranar litinin din data gabata ne Alkalin wata babbar kotu a kasar Mai suna John Bosco ya bayar da umarnin sakin Kizza Besigye a matsayin beli , basa sharadin cewa ci gaba da tsare shi ya sabawa kundin tsarin mulki na kasar.

Kizza Besigye dai na fuskantar laifuffuka ne da suka danganci cin amanar mkasa da gudanar da aiyuka na ta´addanci a hannu daya kuma da yiwa wata mace fyade.

Tuni dai madugun adawa na kasar, wato Kizza Besigye ya karyata wadan nan tuhume tuhume da ake masa da cewa siyasa ce kawai .

A yanzu haka dai Kizza Besigye ya kasance a sahun gaba a adawa da shugaba Yoweri Museveni, a zaben shugaban kasa da aka shirya yi a watan fabarairun wannan shekara da muke ciki.