1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa kan yankin Bakassi

Ibrahim SaniDecember 11, 2007
https://p.dw.com/p/CaLv

Shugaba Umaru Yar´adua na Najeriya, ya buƙaci Majalisar dattijai amincewa da yarjejeniyar da aka cimma da ƙasar Kamaru kan yankin Bakassi. A wata takarda daya aikewa Majalisar, shugaba Yar´adua ya ce shugaba Obasanjo, wanda ya gada ya aike da da ƙudirin ga Majalisar, to amma bai samu tubarrakin ´Yan majalisar ba. Umaru Yar´adua ya yi amfani da wannan damar, wajen miƙawa majalisar ƙudirin don neman amincewarsu. A shekara ta 2006 ne shugaba Obasanjo ya rattaba hannu kann mika yanƙin na Bakassi ga ƙasar ta Kamaru. Hakan kuwa ya biyo bayan hukuncin Kotun ƙasa da ƙasa ne dake birnin Hugue, a shekara ta 2002. A ´yan makonni kaɗan da su ka gabata, majalisar dattijan ta Najeriya ta ce da sake, dangane da matakin miƙa yankin na Bakassi. A cewar Majalisar an miƙa yankin ne ba tare da amincewarsu ba. Hakan a cewar majalisar, abune da ya yi karan tsaye ga dokokin ƙasar.