Harkokin siyasar kasar Masar
February 10, 2005A farkon wannan shekara daukacin ´yan kasar Masar sun yi fatan ganin sauye-sauyen siyasa da yawa a cikin kasar, musamman bayan rantsad da sabuwar gwamnati karkashin FM Ahmed Nazif a lokacin bazara na bara. Shi dai Nazif matashi ne sabon jini wanda ya yi karatun jami´a a kasar Kanada. Hakazalika majalisar ministocinsa ta kunshi hanshakan ´yan kasuwa masu neman sauyi.
A cikin watan oktoban bara ne kuma hukuma ta amince da kafuwar wata sabuwar jam´iya mai suna El-Ghad, wadda ta kasance mai sassaucin ra´ayi kuma amintacciya ga matasa. Shi yasa ba abin mamaki ba ne da a cikin lokaci kankane jam´iyar ta samu dubban magoya baya. A cikin wannan watan ne kuma daruruwan masu ilimi da kuma ´yan adawan kasar suka amince da wani kuduri wanda a ciki suka nuna bukatar bawa jama´a damar zaben shugaban kasa tare da kayyade wa´adin shugabancinsa.
Sannan a karon farko hukumomin kasar sun bawa ´yan adawa da shugaba Hosni Mubarak wanda ya shafe shekaru 25 akan karagar mulki, izinin yin zanga-zangar kin lamirin gwamnati. A farkon watan janerun wannan shekara kuma ´yan takarar shugaban kasa da dama sun yi rajista a kuri´ar raba gardama da ake shirin yi a karshen shekara. Sannan a cikin wani jawabi da yayi a ranar 9 ga watan janeru shugaba Mubarak yayi lale marhabin da ´yan takarar da suka nuna sha´awar shiga cikin wannan zabe.
To amma wai shin ko hakan na nufin kenan iskar canji ta fara kadawa a fagen siyasar kasar ta Masar kamar yadda wasu suka dade suna bege? Ba a kuwa dade ba sai murna ta koma ciki musamman ga ´yan adawa. Domin a jajibiren zaben Iraqi lokacin da shugaba Mubarak ke kan hanyar zuwa Nijeriya don halartar taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, ya sanar da cewar ba zai yarda a gudanar da wata kuri´ar raba gardama da zata ba da damar yin zaben shugaban kasa ba, domin tsarin da kasar ke bi yanzu shine mafi a´ala kuma mafi dacewa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin kasar ta Masar.
A ma halin da ake ciki hukumomin kasar na ci-gaba da tsare ´yan adawa, musamman shugabannin sabuwar jam´iyar nan ta Al-Ghad. Wasu masharhanta dai na da ra´ayin cewa ba za´a samu wani canji a tsarin mulki irin na kama karya a Masar ba. Hasali ma daukacin al´umar kasar sun fi damuwa ne akan neman abin sakawa bakin sallati maimakon mayar da hankali akan al´amuran siyasa. Bugu da kari dukkan jam´iyun kasar ciki har da ta gwamnati da kuma na ´yan adawa ba su da fari jini. Hatta jam´iyar ´yan´uwa musulmi ta Muslim Brotherhood wadda ta yi tashe a cikin shekarun 1990, yanzu haka talakwan kasar sun juya mata baya.
Wani abin da ake fargaba yanzu haka dai shine shugaba Mubarak mai shekaru 76 a duniya ka iya nada dansa wato Jamal wanda masani ne a harkar zuba jari na bankuna, a matsayin wanda zai gajeshi a mukamin shugaban kasa.