1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin sufuri a Jamus sun dawo yadda su ke a da

Ibrahim SaniNovember 17, 2007
https://p.dw.com/p/CIK6

Matuƙan jiragen ƙasa a Jamus sun dawo bakin aiki, bayan yajin aikin awowi 62 . Yajin aikin a cewar rahotanni ya haifar da tsaiko, a harkokin zirga -zirgar fasinjoji a gurare daban daban a ƙasar. Har ila yau yajin aikin ya kuma yi sular asarar miliyoyin Yuro ga Gwamnatin ƙasar.Duk da cewa tattaunawar shawo kan matsalar direbobin na ci gaba da gudana a tsakaninsu da mahukunta, ƙungiyyar ƙwadagon ta yi kurarin shiga wani yajin aikin, a mako mai zuwa.Ƙungiyyar kwadagon ta ce za ta kira wani yajin aikin, matukar ba a cika sharruɗan data gabatar ba. Ƙungiyyar ƙwadagon dai na neman ƙarin albashine ga ma´aikatan.