1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin sufuri na fuskantar barazana a Jamus

Ibrahim SaniDecember 20, 2007
https://p.dw.com/p/CeIH

Ƙungiyyar direbobin jiragen ƙasa a Jamus tayi kurarin shiga wani sabon yajin aiki, a ranar 7 ga watan Janairun sabuwar shekara. Kafin wannan gargadi, a baya ƙungiyyar ta GDL ta gudanar da yajin aiki na kwanaki da dama daga lokaci izuwa lokaci. Matakin ƙungiyyar ta GDL ya haifar da munmunan tsaiko a sufurin jiragen ƙasa a Jamus. Hakan a cewar rahotanni ya haifarwa Jamus asarar Yuro miliyan 75. A wata tattaunawar sulhu a tsakanin ƙungiyyar ta GDL da kuma Kamfanin jiragen ƙasa na Deusche Bahn, a jiya laraba ɓangarorin biyu su tashi ba tare da cimma wata matsaya guda ba. Ƙungiyyar ta GDL na ɓukatar ƙarin kashi 31 cikin ɗari ne na albashi ga direbobin jiragen ƙasan.