1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin tsaro a Britaniya

May 24, 2006
https://p.dw.com/p/Buwz

Wani gagarumin farmaki da yan sandan Britaniya suka ƙaddamar a manyan biranen kasar, sun baiyana nasarar cafke mutane takwas waɗanda ake zargi da hannu a ayyukan taáddanci a kasashen ketare. Biyu daga cikin mutanen an tsare su ne bisa zargin ayyukan tarzoma, yayin da ragowar mutane shidan ake tuhumar su da laifukan da suka shafi harkokin shige da fice. An gudanar da kamen ne a biranen Manchester da London da kuma Liverpool. An ruwaito cewa ɗaya daga cikin mutanen da aka kama ɗan wata ƙungiya ce ta masu gwagwarmayar Jihadi dake ƙasar Libya kuma jamií dake yawon tattara kuɗaɗe ga yan taádda na ƙungiyar al-Qaída.