1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HARKOKIN TSARO A GARIN FALLUJA:

November 8, 2004

sojin amurka na gudanar da sintiri a garin falluja na kasar iraqi.

https://p.dw.com/p/Bver
Hoto: AP

Ya zuwa yanzu dai harkokin tsaro a iraqi,musanmamma a Falluja sun dagule hui da aniya,wanda hakan yasa dakarun sojin kasar Amurka suka dinga ruwan bama bamai a garin Falluja.

Bayanai dai daga garin na falluja sun shaidar da cewa daukar wan nan mataki daga dakarun sojin na Amurka ya biyo mummunan dauki ba dadi ne daya wanzu a tsakanin sojin na Amurka da kuma yan fadan sari ka noke da kuma na kwanton bauna dake garin na Falluja.

Rahotanni dai a yanzu haka sun nunar da cewa dakarun sojin Amurka kusan dubu ashirin ne sukayiwa yankin da yan fadan sari ka noken suke kawanya,a wani mataki na yi musu kafar rago.

Sakamakon kuwa irin wan nan dauki ba dadin dake faruwa a tsakanin wadan nan bagarori biyu,a yau litinin Abu musab Al zarqawi ya aike da wata sanarwa izuwa hanyar sadarwa ta gizo gizo,inda yake bukatar musulmin kasar su tashi tsaye tsaiwar daka wajen yakar sojojin taron dangin dake kaiwa garin na Falluja hare haren bama bamai.

Sanarwar taci gaba da cewa da yardar Allah tare da taimakon musulmi sai yan kungiyyar sa sun ga bayan dakarun mamayen dake cin karen su babbu babbaka a fadin kasar ta iraqi baki daya.

Bugu da kari shugaban kungiyyar ta Alqeeda dake kasar ta iraqi ya kuma soki lamirin malaman kasar wajen kin bawa kungiyyar sa goyon baya na fatattakar sojojin mamayen daga iraqi da cewa suma basu da maraba da sojojin mamayen,wato a takaice dai danjuma ne da kuma danjumai.

Wan nan dai kira na Abu Musab Al zarqawi yazo ne a dai dai lokacin da dakarun sojin mamayen ke jiran umarni na afkawa garin na Falluja da yaki bisa manufar kwato garin daga hannun musulmi masu tsattauran raayi dake garin.

A waje daya kuma yayin da ake cikin wan nan hali a can kuma birnin Bagadaza mutane shida ne suka rasa rayukan su wasu kuma da dama suka jikkata ciki kuwa har da sojan Amurka daya.

Wan nan al,amari dai ya faru ne yayin da yan fadan sari ka noke na birnin suka kai wani hari kann sojojin na Amurka a yau litinin a can tsakiyar birnin na Bagadaza.

A can kuma garin Ramadi Bom ne ya tashi a cikin wata karamar mota wanda hakan yayi ajalin mutane hudu a hannu daya kuma ya jikkata mutun guda.

A daya hannun kuma a can ma garin Mosul wani bom nya tashi da motar dake dauke da dakarun sojin na Amurka a kann hanyar su ta zuwa tsakiyar birnin,wanda hakan yayi sanadiyyar jiwa soji daya rauni a cewar kakakin rundunar sojin ta Amurka.

Har ilya yau dai a can Garin Samarra rahotanni sun shaidar da mutuwar wadan su yan iraqi biyu dakewa kamfanin Amurka aiki wasu kuma biyu sun samu raunuka.

Hakan kuwa ya faru ne yayin da aka kawo musu hari yayin da suke cikin motar su a cewar jamian yan sanda na kasar.

Bayanai dai sun tabbbatar da cewa bisa ire iren wadan nan abubuwa dake faruwa ya haifar faraministan kasar ta iraqi Iyad Alawi ya saka dokar ta baci a kusan da dama daga cikin garurun kasar ta Iraqi in banda garuruwan dake dauke da kurdawa a cikin su,wanda mafiya yawan su sunfi karfi ne a arewacin kasar ta Iraqi.

A cewar Iyad Lawi gwamnatin tasa ta dauki wan nan matakin ne a sabili da inganta harkokin tsaro na fadin kasar baki daya musanmamma bisa la,akaei da cewa lokacin zabe na kara karatowa.

Ibrahim Sani.