1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin zaman lafiya sun fara inganta a Lebanon

August 16, 2006
https://p.dw.com/p/BumX

Rahotanni daga yankin gabas ta tsakiya na nuni da cewa daftarin sulhun da Mdd ta gabatar, a game da rikicin Israela da kungiyyar Hizboullah na nan na aiki yadda yakamata.

Kafafen yada labarai dai sun rawaito, janar Alain Pellegrini, daya daga cikin kwamandan dakarun Mdd a kudancin Lebanon, na tabbatar da wannan batu.

Ya zuwa yanzu dai Mdd tace zata kara yawan dakarun kiyaye zaman lafiyar nata a kudancin kasar ta Lebanon izuwa dubu 3 da dari 5 daga nan izuwa makonni biyu masu zuwa.

Mdd ta ci gaba da cewa ,zata yi hakan ne don tabbatar da cewa dakarun sun maye gurbin dakarun kiyaye zaman lafiyar Israela dake Jibge a gurin, don ci gaba da tabbatar da doka da kuma Oda, bayan tafiyar su.

A nan gaba dai a cewar mataimakin Kofi Anan, wato Hedi Annabi, Mdd zata kara yawan dakarun sojin kiyaye zaman lafiyar a kasar ta Lebanon izuwa dubu goma sha biyar.

Kasashe irin su Faransa da Turkiyya da Malaysia tuni suka bayyana aniyar su na taimakawa da sojojin da zasu yi aiki a laimar ta Mdd a kasar ta Lebanon.