1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hasina ta bukaci Myanmar ta karbi yan Rohingya

Abdullahi Tanko Bala
September 12, 2017

Firaministar Bangaladesh Sheikh Hasina ta yi alkawarin gudunmawar abinci da matsugunai ga yan kabilar Rohingya marasa rinjaye da suka yi gudun hijira zuwa Bangladesh

https://p.dw.com/p/2jp7a
Bangladesch Sheikh Hasina im Flüchtlingslager Kutupalong
Hoto: picture-alliance/AP/S. Kallol

Firaministar Bangaladesh Sheikh Hasina ta yi kira ga kasar Myanmar ta karbi yan Rohingya da suka yi gudun hijira domin tserewa rikicin kabilanci da ya barke a kasar a ranar 25 ga watan Augustan da ya gabata.

Hasina ta kuma yi kira ga kasashen duniya su kara matsa kaimi kan Myanmar na tabbatar da tsaron yan Rohingya ta na mai cewa ba za'a lamunci irin wannan rashin adalcin ba.

Sai dai kuma rahotanni sun ce kasar ta Myanmar ta dasa nakiyoyi akan iyakoki ta kuma sanar da yan Rohingyan cewa sai sun nuna takardar shaidar cewa sun yan Myanmar ne kafin a barsu su koma.

A waje guda kuma Majalisar Dinkin Duniya ta fara aikin jigilar agaji ga musulmin yan Rohingya dubu 370 wadanda suka yi gudun hijira zuwa Bangladesh.

Jirgin farko na kayan agajin ya kai ton 91 zuwa Cox Bazar da ke kan iyakar jihar Rkhine da ke fama da tarzoma a Myanmar.